Za a iya ɗaure masu ɗaukar ma’aikata suna biyan ƙasa da N70,000 —Gwamnati
Mafi ƙarancin albashi ga ma’aikaci a Najeriya ya kamata ya samu N70,000,
Gwamnatin Tarayya ta yi kira ga kamfanoni masu zaman kansu da su bi tsarin mafi ƙarancin albashi na N70,000, inda ta yi gargaɗin cewa ba za ta amince da saɓanin hakan ba.
A cewar Gwamnatin Tarayya, sabon mafi ƙarancin albashi ya zama dole don magance yanayin tattalin arzikin da ake ciki a halin yanzu.
Ya jaddada cewa babu wani ma’aikacin Najeriya, ko yana aikin gwamnati ko na kamfani mai zaman kansa da za a biya ƙasa da mafi ƙarancin albashin.
Babban sakataren Ma’aikatar Ƙwadago da Samar da Ayyukan Yi ta Tarayya, Ismaila Abubakar, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin da yake jawabi a wajen taron shekara-shekara na ƙungiyar ma’aikata na ma’aikatu masu zaman kansu na Najeriya karo na 13, wanda aka gudanar a Ikeja, a jihar Legas.
Abubakar wanda ya samu wakilcin Daraktan Ɗaukar Ma’aikata da Albashi na ma’aikatar, John Nyamali, ya ce, “A yanzu mafi ƙarancin albashi ya zama doka, saboda haka, laifi ne da ke da hukunci ga duk wani mai ɗaukar ma’aikaci ya biya ƙasa da N70,000 ga kowane ma’aikacinsa.
“Hukumomin ɗaukar ma’aikata masu zaman kansu su sanya hakan ya zama wajibi a duk wata kwangila da za su karɓa daga hannun masu ɗaukar aiki cewa kada ma’aikatansu su riƙa samun ƙasa da mafi ƙarancin albashi.
“Mafi ƙarancin albashi ga ma’aikaci a Najeriya shi ne N70,000, kuma ina ganin ya kamata ya samu hakan bayan an cire adadin da za zaftare.”