Za a iya kawar da barace-baracen almajirai idan…. – Maja bakin Sheikh Xahiru Bauchi
Sidi Ali Sise Xahiru Bauchi, ya taba rike mukamin Darakta Janar na Hukumar Kula da Makarantun Allao (Tsangaya) ta Jihar Bauchi, kuma yanzu haka shi ne Daraktan Harkokin Ilimi na Makarantun Sheikh Xahiru Bauchi. Sidi Ali Sise malami ne da ya kware a kan dukan kira’o’in Alkur’ani. Ya yi karatu a Jami’ar Azhar da ke […]
Sidi Ali Sise Xahiru Bauchi, ya taba rike mukamin Darakta Janar na Hukumar Kula da Makarantun Allao (Tsangaya) ta Jihar Bauchi, kuma yanzu haka shi ne Daraktan Harkokin Ilimi na Makarantun Sheikh Xahiru Bauchi. Sidi Ali Sise malami ne da ya kware a kan dukan kira’o’in Alkur’ani. Ya yi karatu a Jami’ar Azhar da ke Masar, kuma ya yi karatu a kasar Saudiyya. Sannan shi ne ke ja wa mahaifinsa Sheikh Xahiru Usman Bauchi baki lokacin tafsiri. A zantawa da manema labarai a Bauchi ciki har da wakilinmu, ya fayyace dalilan yin almajiranci da yadda za a inganta almajirancin har ma almajirai su daina yin bara da kansu:
Allah gafarta Malam ga shi gwamnati na kokarin yin wani shiri domin tallafa wa makarantun Alkur’ani a karkashin Hukumar UBEC me za ka ce?
Alhamdulillahi abu ne in lokacinsa ya yi dole a yi shi. Kamar harkar ilimi a nan Arewa ana magana da yawa cewa an bar mu a baya Kudu sun yi gaba, sun yi abubuwa da yawa mu kuwa da saura. Sai aka duba aka ga marantunmu na addini ne aka mai da su kamar ba masu amfani ba, ba a kulawa da su, har Allah Ya kawo mu lokacin da aka duba aka ce su ma wadannan makarantu namu suna da amfani domin ilimi mai tarin yawa ake koyarwa a ciki, ya kamata a kula da su. Sai gwamnati ta ga ya kamata ta sa hannu ko za a farfado da wadannan makarantu shi ne aka tuntube mu, wannan kuma shi ne tuntuba ta farko da gwamnati ta yi cewa yaya yanayin makarantunmu saboda tana so ta shigo ta taimaka. Wannan ya sa muka ji dadi muka yi godiya ga gwamnatin in dai da gaske suke yi insha Allahu za su samu abin da suke nema tun da sun biyo ta kofofin da suka kamata,
Me za ka ce kan batun almajiranci a garuruwa da ake cewa yana ci wa wa jama’a tuwo a kwarya?
Alhamdulillahi ai yanzu almajirancin ya zamo har wadanda ba almajirai ba ne sun zama almajirai, kowa ya zamo almajiri saboda halin da kasar take ciki a yanzu. Amma in gwamnati ta yi da gaske kuma al’umma suka tsaya aka sa ikhlasi an dauko hanyar da za a yi maganin abubuwan kwarai da gaske. Saboda yawanci abubuwan da ake ganin kamar almajirai ne suke yi gaskiya ba ainihin almajirai na gaskiya ba ne sai dai wadanda suka shiga cikin rigar almajirancin. Domin asalin almajiran ba su ne suke aikata wasu abubuwa na assha da ake gani ba, zan iya tunawa lokacin da muke cikin gwamnati muke maganar almajirai, yawancin yaran da muke samu suke kwana a tasha ko suke yawo kwararo-kwararo suna aikata abubuwan da ake ke cewa ba kyau in muka bincika in ka ji labarinsu sai ka ga kai ma ba abin da ka iya, ban da ka bar su haka su ci gaba da yin abin da suke yi, domin ba za ka iya taimaka musu ba. Dalili za ka samu wadansu yaran su ce su marayu ne babansu ya rasu, mahaifiyarsu tana zaune ba wanda yake ba ta abinci sai abin da suka samo a bara. Barar da suke yi ake rainawa din, da ita ce suke samu su ciyar da mahaifiyarsu da kannensu. Don Allah in ka samu irin wadannan yara me za ka ce? Za ka kama su ne, ko za ka musu wani abu? Tunda kai ba ka yi musu yadda za su ci abinci ba dole ka bar su su yi buge-bugensu domin su rayu. Saboda haka ya kamata a rika duba irin wadannan al’amura a rika kulawa da su. Yawancin masu bara ba almajiranci ya sa su ba, tsananin talauci da maraici da rashin gata da matsalolin yau da kullum suka sa mutane da yawa bara ake dora laifin barar da suke yi a kan almajiran da ke neman ilimin Alkur’ani. Kuma babban abin da ya sa nake gani kamar za a iya shawo kan lamarin shi ne a baya idan gwamnati ta yunkuro za ta taimaka ba ainihin masu makarantun take samu ba, yanzu ne aka tuntubi ainihin masu karatun Alkur’ani wadanda suke da almajiran. Ka ga a da ana samun matsala ce za ka ga wadanda sukay i wani karatu daban mu kuma da muka yi karatu namu karatun addini ne sai a ce wanda bai san yaya ake yin karatun addini ba ne zai yi maka alkibla a naka, ko yana gani nakan ba ka iya ba ne, ko kuma shi ne zai koya maka, kuma kai ba ya ganinka da kima shi yana gani ya fi ka komai shi ne zai yi maka. Wannan ne matsalar da suka yi ta samu a baya, amma yanzu da yake sun yi sun yi ba su samu yadda suke so ba, shi ne suka sake tunani suka dawo wajen masu abin in Allah Ya yarda za a ci nasara in dai suka yi da gaske.
Yanzu in gwamnati ta kafa dokar hana bara za ku amince da ita?
Tunda shawara gwamnatin ta ce a ba ta, za mu nuna mata wata hanya da in dai almajiran da ke karatun Alkur’ani ne ake maganar bara a kansu in sun bi shawarar barar da kanta za ta bace, ba sai ta sha wahalar sanya wata doka ba, in dai ta bi hanyar da ta kamata. A taimaka kamar yadda Kudu duk ba wata makarantar da gwamnati ba ta taimakawa a ciki, mu kuwa da yake mun kama karatun addini ana gani makarantunmu kamar makarantu ne da gwamnati ba ta amfana da su, alhali cikin wannan karatun addini da muke yi ba irin gudunmawar da ba mu kawo wa ’yan kasa. Ka ga muna cusa tsoron Allah, muna sanar da sanin Allah muna koyar da dabi’un kirki na gaskiya da adalci da kulla da zumunci da zamantakewa kuma dukan al’ummar Musulmi ’yan kasa suna son karatun addinin don haka wajibi ne a kan gwamnati ta kula da abin da ’yan kasa suke so. Akwai wani abu da ya faru dazu da safen nan akwai wani kauye da muka je an yi rasuwa ne amma abin mamaki an rasa wanda ya iya wankan gawa a garin, to tunda ’yan kasa suna da bukata gwamnati ta yi abin da ’yan kasa suke so, amma sai aka maida ilimin addini ga shi muna bukata amma aka mai da ba ruwansu da wannan abin.
Yaya batun hada karatun boko a makarantun allon?
Alhamdulillahi yanzu mu makarantunmu ana hadawa da ilimin boko, don haka mun kai matsayin duk irin taimakon da gwamnati za ta yi wa makarantar da ke koyar da boko zalla to mu kashi biyu za ta yi mana, amma ko da gwamnati ba ta ga amfaninsa ba ta sa hannu ciki ba tunda mu mun san amfaninsa to muna yi, kuma alhamdulillahi koda taimakonsu ko ba taimakonsu abin na tafiya, kuma mun cimma nasara tunda yanzu a duniya in aka ce ina ne suka kula da Alkura’ni dole za a sa Najeriya a ciki, ka ga ke nan malamanmu sun cimma burinsu nauyin da yake kansu sun sauke, idan gwamnati ta shigo abin zai kara bunkasa, kuma ita ma za a yi mata yadda takeso, za a yi mata karatun bokon da take so. Kuma dama matsalar duk rashin hadin kai ne kamar yadda muka taba tattaunawa a wani taron da muka yi, cewa gwamnati ba ta daukar karatun addini da kima da muhimmanci kuma yawanci ’yan Arewan nan Musulmi ne, kuma shi Musulmi addininsa ya fi masa komai. To tunda yanzu an kimanta karantun addinin insha Allahu masu makarantun ma za su imanta karatun bokon, domin abubuwa ne biyu ga mafi muhimmanci ga kuma muhimmi karatun duniya shi ne muhimmi karatun Lahira shi ne mafi muhimmanci. Mu almajirai muka dauki mafi muhimanci ka ga komai iliminka in ka samu duniya ba ka samu Lahira ba komai ya lalace maka, in kuwa ka samu Lahira ba ka samu duniya ba ba ka rasa komai ba, amma yanzu mun gode Allah za mu hada da muhimmin da mafi muhimmanci don a samu nasara.
A karshe ko akwai wata shawara da za ka bayar?
Alhamdulillahi, shawarata ita ce addini nasiha ne, ina yi mana nasiha da mu da masu mulki da hukumomi da kamfanoni da kungiyoyi da ma’aikatu mu ji tsoron Allah mu yi adalci ga kowa koda wa makiyinmu ne kuma mu fadi gaskiya, mu bai wa duk wani mai hakki, hakkinsa ba tare da la’akari da bambancin siyasa ko ra’ayi ba. Wato wani abu ne ya faru wata rana a Kaduna aka ba da lambobin yabo ga wadanda suka taimaka wa Alkur’ani da aka zo wata gaba sai sunayen wadansu wadanda suka yi taimako ya shigo cikin wadanda za a bai wa lambar yabon sai siyasarsu ta zama ta bambanta da ta gwamnatin, sai aka ce a cire sunansu. Ina gani haka ba adalci ba ne mutumin da ya gina makarantun tsagaya fiye da 50 gini irin na zamani da na’urorin kwamfuta, ya tallafi almajirai yaya don ya saba da ra’ayi ko siyasa za a ce a cire shi a ciki? Na jawo ayoyin Alkura’ni guda biyu da suke magana a kan gaskiya da adalci a wajen taron. Allah Ya taimake mu Ya ba mu lafiya da zama lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya Allah Ya saukar da alheri a Najeriya Allah Ya yaye sharri a Najeriya.