Za a iya kawar da siyasar ubangida a Legas – El-Rufa’i

A Jihar Legas da jihohin Kudu maso Yamma siyasar ubangida na da matukar tasiri a siyasar yankin inda ake da wadansu mutane da suke ruwa-da-tsaki wajen nada gwamnoni da masu rike da madafun siyasa, ubangidan siyasa mai matukar tasiri a yankin shi ne tsohon Gwamnan Jihar Legas kuma Jagoran Jam’iyyar APC ta Kasa, Cif Bola Ahmed […]

Za a iya kawar da siyasar ubangida a Legas – El-Rufa’i

Nasir El-Rufai, Gwamnan Jihar Kaduna

A Jihar Legas da jihohin Kudu maso Yamma siyasar ubangida na da matukar tasiri a siyasar yankin inda ake da wadansu mutane da suke ruwa-da-tsaki wajen nada gwamnoni da masu rike da madafun siyasa, ubangidan siyasa mai matukar tasiri a yankin shi ne tsohon Gwamnan Jihar Legas kuma Jagoran Jam’iyyar APC ta Kasa, Cif Bola Ahmed Tinubu da yanzu tasirinsa ya  zarce jihohin Kudu maso Yamma ya fara ketarewa zuwa jihohin Arewa.

Wani abu da ya dauki hankalin jama’ar jihar shi ne kalaman da Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i ya yi a ranar Asabar  da ta gabata lokacin da yake jawabi a wani taro da ya halarta a Legas ya ce za a iya kawo karshen siyasar ubangida a Legas kamar yadda ya kawo a Jihar Kaduna.

A cewar Gwamna El-Rufa’i a baya a Jihar Kaduna akwai wadansu mutum 3 zuwa 4 wadanda idan ba su tsaya wa mutum ba, bai isa ya zama Gwamnan Kaduna ba, “A wannan lokacin dole ka bi su ma’ana ka yi musu biyayya ka yi ta musu hidima domin ka samu yardarsu, daya daga cikinsu ma ya taba yi min gorin shi ya kawo ni na zama Gwamna kuma wai a cewarsa shi zai cire ni,” inji shi.

Ya ce, hanya mafi sauki ta kawar da tsarin siyasar ubangida shi ne tuntubar jama’a kai-tsaye, “Idan ka kulla kyakyawar alaka da jama’a wadanda suke yin zabe za ka yi nasarar kawar da siyasar ubangida amma yin hakan na bukatar lokaci da juriya tare da jajircewa, za ka kwashe akalla shekara 3 zuwa 4 kana kokarin kulla alaka,  don haka idan akwai wanda ke son tsayawa takarar Gwamna a Legas a shekarar 2023 kuma yake son kawar da siyasar ubangida sai ya fara shiri tun yanzu,” inji shi.

Gwamna El-Rufa’i ya  ce, a Jihar Legas mutum miliyan 5 ne suka karbi katin zabe kafin zaben bana,  amma mutum miliyan daya ne kacal suka yi zaben Gwamna,  don haka hanya mafi sauki wajen kawar da siyasar ubangida ita ce a tuntubi ragowar mutum miliyan 4 da ba su kada kuri’arsu ba,  “Idan zan tsaya takarar Gwamnan Legas abin da zan yi zan tuntubi wadannan mutum miliyan 4 da ba su yi zabe ba, in kulla kyakyawar alaka da su, sannan in shawo kan akalla mutum miliyan 2 su zabe ni,  idan na yi haka na kawar da siyasar ubangida,” inji shi.