‘Za a iya kawo karshen cutar kanjamau kafin shekarar 2030’
Majalisar dinkin Duniya ta ce yawan mutanen da ke kamuwa da kuma mutuwa sanadiyyar cutar kanjamau na raguwa a kullum, wanda hakan ke nufin cewa ana samun nasara a yakin da ake da cutar kuma za a iya kawo karshenta a duniya kafin shekaru 16 masu zuwa.A wata sanarwa gabanin babban taron kan cutar da […]
Majalisar dinkin Duniya ta ce yawan mutanen da ke kamuwa da kuma mutuwa sanadiyyar cutar kanjamau na raguwa a kullum, wanda hakan ke nufin cewa ana samun nasara a yakin da ake da cutar kuma za a iya kawo karshenta a duniya kafin shekaru 16 masu zuwa.
A wata sanarwa gabanin babban taron kan cutar da majalisar ta shirya gudanarwa mako mai zuwa a birnin Melbourne na kasar Australiya, ta ce ba kamar yadda aka saba gani ba a baya, akwai kyakkyawan fatan ganin bayan cutar. Har lia yau sanarwar ta ce idan aka tsaya da yakarta ko kuma aka ki daukar wani gagarumin mataki, cutar ba za ta kawo karshe ba.
An bayyana cewa yawan wadanda suke kamuwa da cutar bai karu ba daga mutane miliyan 35 a fadin duniya. Cutar mai karya garkuwar jiki, ta yi ajalin mutane miliyan 39, cikin mutane miliyan 78 da suka harbu da ita tun daga farkon shekarar 1980.
Tun a shekara ta 2001 yawan masu dauke da cutar ya fara ja baya da kashi 38 cikin 100. Hakazalika, tun daga shekarar 2005 ne aka fara ganin raguwa wajen yawan wadanda suke mutuwa sanadiyyar cutar, inda ya ragu zuwa kashi 35 cikin 100.