Za a iya rasa ruwa baki daya a birnin Cape Town na Afirka ta Kudu
Bayan fama da fari da ba a taba samu ba a cikin shekara 100 da suka wuce, hukumomi a kasar Afirka ta Kudu sun gargadi mazauna birnin Cape Town da ke Afirka ta Kudu da su adana ruwa a duk inda za su iya adana shi. Inda suka ce idan har ba a samu ci […]

Bayan fama da fari da ba a taba samu ba a cikin shekara 100 da suka wuce, hukumomi a kasar Afirka ta Kudu sun gargadi mazauna birnin Cape Town da ke Afirka ta Kudu da su adana ruwa a duk inda za su iya adana shi. Inda suka ce idan har ba a samu ci gaba ba nan da 21 ga watan Afrailu, fanfuna da yawa za su daina bayar da ruwa. Wanda hakan ke nufin cewa ko ruwan wanka ma sai an sha wahalar gaske kafin a samu, kamar yadda CNN ta ruwaito.
CNN ta ruwaito cewa akalla mutum na bukatar lita 75 na ruwa domin wanka, amma idan har ba a shawo kan wannan lamarin ba, da kyar mutum zai samu lita 25 na ruwan a rana.
Haka nan kuma an umarci manona da su rage amfani da ruwa da akalla kashi 60, sannan kuma ‘yan kasuwa da suka ki bin umarnin za su fuskanci fushin hukuma, ko kuma a sanya na’urar da za ta rika kula da yadda ake amfani da ruwa.
Wani mai kiwon dawaki a Afirka ta Kudu mai suna Ross Kieswetter ya shaida wa CNN cewa, “Wannan lamari ne mai wahalar gaske,”
Haka nan kuma jami’ai sun bukaci jama’a su takaita yin amfani da ruwa wajen kora ba-haya don adana ruwan kamar yadda BBC ta ruwaito.
Shugaban gwamnatin yankin ta ce, idan aka samu daukewar ruwa a famfuna “Annobar da za ta biyo baya ta wuce wadda muka taba fuskanta.”
Helen Zille ta ce har yanzu akwai yiyuwar kauce wa daukewar ruwa ta wuni guda.
Ta kuma ce za a ci gaba da kau da kai daga matsalar idan kowane mutum yana amfani da ruwa lita 50 ko kasa da haka a kowane yini.
“Wannan ba abu ba ne mai wahala idan muka sa hakan a ranmu wajen yin amfani a gidajenmu da wuraren aikinmu,” inji ta.
Mis Zille ta bayar da wasu shawarwari kan yadda za a adana ruwa.
“Ku kashe mazubin ruwan bandakunanku, ku rika amfani da ruwan da kuka yi wanki wajen kora ba-haya, kuma ku rika tara ruwan wankin kuna amfani da shi a bandakin maimakon zubarwa”.
Ta kara da cewa,”A halin da ake ciki yanzu ba wanda zai iya samun damar yin wanka sama da sau biyu a mako. Akwai bukatar adana ruwa tamkar a kansa rayuwarka ta ta’allaka”.
A bara, Mis Zille ta bayyana cewa sai bayan kwana uku-uku take wanka.
Birnin Cape Town ya shahara da zuwan masu yawon bude ido, amma yana fuskantar matsanancin fari na tsawon lokaci.
Yawancin ‘yan Afirka ta Kudu sun farfado daga wahalar farin da suka fuskanta wanda dumamar yanayi ya haddasa.