Za a iya sayar da litar mai naira 30 – danladi Fasali

Alhaji danladi Garba Fasali shi ne babban sakataren kungiyar dillalan mai masu zaman kansu ta kasa. A wannan tattaunawar da ya yi da wakilinmu ya bayyana yadda za a magance matsalar man fetur da ake fama da ita a Nijeriya, tare da bada tabbacin cewa nan bada dadewa ba mai zai wadata a kasar nan. […]

Za a iya sayar da litar mai naira 30 – danladi Fasali
Za a iya sayar da litar mai naira 30 – danladi Fasali

Alhaji danladi Garba Fasali shi ne babban sakataren kungiyar dillalan mai masu zaman kansu ta kasa. A wannan tattaunawar da ya yi da wakilinmu ya bayyana yadda za a magance matsalar man fetur da ake fama da ita a Nijeriya, tare da bada tabbacin cewa nan bada dadewa ba mai zai wadata a kasar nan. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Aminiya; Wadanne dalilai ne kake ganin suka kawo matsalar man fetur a kasar nan?

danladi Fasali; A gaskiya dalilan da suka kawo karancin man da ake fama da shi a kasar nan a halin yanzu shi ne matsala ce da wannan sabuwar gwamnatin ta gada daga tsohuwar gwamnatin da ta gabata, domin kowa ya sani cewa gwamnatin da ta shude ta jawo matsaloli iri-iri saboda rashin gaskiya a kan harkokin mai a kasar nan. Domin duk abin da za a yi a gwamnatin da ta gabata babu gaskiya a cikinsa.
Na farko dai kowa yana da labarin yadda aka rika amfani da shigo da tataccen man fetur daga kasashen waje aka rika sace kudaden kasar nan. Irin wadannan matsaloli da wannan sabuwar gwamnati ta gada daga gwamnatin da ta gabata sune suka kawo mu ga wannan hali da muke ciki na matsalar mai a kasar nan.
Kuma a zaben da ya gabata jama’ar Nijeriya sun yi wani juyin juya hali a Nijeriya. Dama duk kasar da aka ce an yi juyin juya hali dole a samu irin wadannan matsaloli wadanda sai a hankali za a magance su. Amma babbar matsalar da ake ciki ita ce, kamfanonin da suke shigo da tatatcen man fetur daga kasashen waje an sa sun karbi kudaden bankuna sun sayo mai daga kasashen waje, maimakon a biya su kudadensu sai aka ki, aka yi amfani da wadannan kudade wajen yakin neman zaben da ya gabata.
Kuma saboda gwamnatin da ta gabata ta ki ta gyara matatun man kasar nan kuma ta ki yarda ta bai wa ‘yan kasuwa dama su bude sababbin matatun mai a kasar nan. Domin kungiyarmu sama da shekara guda ke nan muka kawo turawa daga kasashen waje suka zo da kudadensu kusan dala biliyan 5 suna son su gina matatun mai a kasar nan. A matsayinmu na ‘yan kasa mun yi kokari mun samar masu da wuraren da suke so. Sun ce suna son su bude a Arewa mun samar musu da wuri a jihar Kogi, saboda tana kusa da ruwan da aka jawo kuma akwai mai a bangaren. Sannan mun samu wuri a jihar Bayelsa. Amma ina mai tabbatar maka cewa gwamnatin da ta gabata ta kasa bada hadin kai, ba a tsaya an saurari wadannan turawa ba.
Kuma ka san cewa an kashe matatun man kasar nan, matatar mai ta Kaduna fiye da shekara daya ba ta aiki, matatun mai na Fatakwal da Warri dukkansu aikin da suke yi bai taka kara ya karya ba. Kuma duk kasar da ba ta da matatun mai dole ne ta dogara da shigowa da mai daga kasashen waje. Wadannan sune matsalolin da suka dabaibaibaye harkar mai a Nijeriya.
Amma sanatoci sun shigo cikin wannan maganar, sun kira mu kuma mun tabbatar masu cewa a matsayinmu na dillalan mai za mu taimaka don kawar da wannan hali da muke ciki a kasar nan.
A yanzu ina mai tabbatar maka cewa mun samu mashala da gwamnati kuma ta yi mana alkawari za ta biya mu kudaden da muke bi.
Aminiya; Wato kana nufin wannan sabuwar gwamnati za ta warware wannan matsala?
danladi Fasali; Babu shakka wannan sabuwar gwamnati ma ta warware wannan matsala ta karancin mai a kasar nan. Domin a yanzu maganar nan da muke yi da kai, mun gaya wa dukkan ‘yayan kungiyarmu da gidajen manmu kan mu cigaba da aiki. Don haka muna rokon ‘yan sanda su ba mu kariya saboda a rika sayar da mai a gidajen manmu dare da rana. Kuma mun kafa kwamiti na musamman wanda yake lura da man da ake turawa, mun tura motoci zuwa Legas don a kawo mai ko’ina a cikin kasar nan. Don haka ina tabbatar maka cewa idan Allah Ya yarda nan bada dadewa ba za a daina ganin layukan motoci a gidajen mai.
Sannan kuma a cikin shirin gaggawa da kungiyar take yi, muna neman gwamnati ta bamu goyan baya. Mun yi magana da turawan nan namu da suke son su bude matatun mai a kasar nan. Kuma sun tabbatar mana cewa idan za a zauna a samu wata yarjejeniya ta musamman da gwamnati da mu da su wadannan turawan za su kawo man fetur da kananzir da gas nan Najeriya ba tare da tallafin kudin gwamnati ba. Kuma za su sayar kamar yadda gwamnati take son a sayar. Wannan wani shiri ne na gaggawa kafin gwamnati ta ba mu dama mu kafa matatun mai a kasar nan.
Kuma idan gwamnati ta ba mu hadin kai akwai matatun mai na gaggawa wadanda za a iya yinsu a cikin watanni 6. Akwai kuma babbar matatar mai wadda za a iya yinta a cikin watanni 18. Don haka muna son za mu je mu kai abubuwan da muke bukatar a taimaka mana. Idan gwamnati ta yarda da wadannan bukatu namu, za mu malala man fetur da kananzir a ko’ina a Najeriya Kuma mu sayar ba tare da gwamnati ta biya ko sisin kwabo ba na tallafi. Wannan zai kawar da maganar tallafin da ake ta magana a kai wanda ake badakala a kansa.
Ba mu da wata mafita kan wannan hali da muka shiga a Najeriya sai gwamnati ta gyara matatun kasar nan ta kuma bai wa ‘yan kasuwa dama suma su kafa matatun mai masu zaman kansu. Wannan ita ce hanyar da gwamnati za ta bi ta warware matsalar mai a kasar nan.
Idan aka baiwa ‘yan kasuwa dama suka kakkafa matatun mai a kasar nan, sai an sayar da litar mai naira talatin. Domin ‘yan kasuwa zasu fara gasa a tsakaninsu kamar yadda kamfanonin wayar sadarwa suke yi a tsakaninsu. Domin a farkon fitowar layin waya, kamfanin wayar sadarwa na MTN ya sayar da layinsa kusan naira dubu 100, ya dawo naira dubu 50, ya dawo naira dubu 30 ya dawo naira dubu 10, a yanzu ma suna son mutum ya saya ne ma a ba shi kyauta. Saboda yanzu akwai kamfanonin wayar sadarwa da yawa a kasar nan.
Saboda haka ina tabbatar maka idan aka gyara matatun man kasar nan aka kuma bai wa ‘yan kasuwa dama suka kafa mamatun mai masu zaman kansu, sai an zo ana sayar da litar mai naira talatin a kasar nan kamar yadda na fada.
Aminiya; To mene ne kake ganin ya sanya gwamnatin da ta gabata ba ta dauki irin wannan matakin ba don magance wannan matsala?
danladi Fasali; Ai gwamnatin da ta gabata ba gwamnati ce da take da manufar gyara kasa ba. Gwamnati ce ta wasu tsiraru da suke son su hallaka kasar.
Aminiya; To a karshe, wannan sako ko kira ne kake da shi zuwa ga dukkan masu hanu kan harkar mai a kasar nan?
danladi Fasali; To yanzu duk mai hankali ya san cewa an samu canji a kasar nan. Domin dama abin da kowa yake nema shi ne Allah Ya kawo canji, mai gaskiya ya shiga. Don haka kowane dan kasuwa da yake da hannu a kan harkar mai ya daura damarar yin gaskiya a cikin wannan harka, ta yadda shi ma zai kawo gudunmawa don a gyara wannan harka.