Za a iya siyasa ba tare da ’yan banga ba – Hauwa El-Yakub
Hajiya Hauwa Ibrahim El-Yakub ’yar takarar sanata ce a mazabar Kano ta tsakiya karkashin Jam’iyyar NPM, a tattaunawarta da Aminiya ta ce siyasa tana iya yiwuwa ba tare da amfani da ’yan banga ba: Aminiya: Me ya ja ra’ayinki kike shiga siyasa? Hauwa El-Yakub: Nakan ce ba siyasa na shiga ba gwagwarmaya nake yi, domin […]
Hajiya Hauwa Ibrahim El-Yakub ’yar takarar sanata ce a mazabar Kano ta tsakiya karkashin Jam’iyyar NPM, a tattaunawarta da Aminiya ta ce siyasa tana iya yiwuwa ba tare da amfani da ’yan banga ba:
Aminiya: Me ya ja ra’ayinki kike shiga siyasa?
Hauwa El-Yakub: Nakan ce ba siyasa na shiga ba gwagwarmaya nake yi, domin duk wanda ya san ni ya san ni a gwagwamarya ta rayuwa ta nema wa jama’a ’yancinsu. Duk gaba dayan ayyukan da na yi a kan hakan ne domin aikina ya shafi samar da ci gaba ga dan Adam. Ban gamsu da yadda gwamnati ke tafiyar da lamura ba, domin idan kika duba yadda fyade da shaye-shayen miyagun kwayoyi da daba a tsakanin matasanmu kullum karuwa suke yi. Ina cikin kungiyoyi da dama da suke kula da irin wadannan matsaloli, sai nake ganin gwamnati ba ta yin kokarin da ya kamata wajen magance matsalolin don haka na ga akwai bukatar mu shigo cikin lamarin. Ni kwararriya ce a kan harkar tallafawa rayuwar dan Adam, na yi aiki da ofisoshin jakadancin kasashen waje daban-daban na yi da Kungiyar Tarayyar Turai (EU) da Majalisar Dinkin Duniya da Hukumar Raya Kasashe ta Birtaniya DFID da sauransu. A lokacin da nake aikin na ga cewa akwai talauci a karkara akwai wani kauye da na dauki shekara sama da 15 ina shiga amma babu wani abu na ci gaban dan Adam a kauyen. Na yi iyakacin kokarina don gwamnati ta taimaka musu amma hakan bai samu ba sai daga baya ne na samu wadansu bayin Allah suka fara yi musu aikin ginin makaranta. Ire-iren wadannan misalai suka sa na ga ya kamata in shiga siyasa don akwai gudummawar da zan iya bayarwa a wannan bangare.
Na fahimci cewa idan har mutanen kirki ba su shiga siyasa ba, to haka za a bar lamarin ya ci gaba da lalacewa.
Aminiya: A ganinki me ya sa ’yan siyasa ke amfani da ’yan daba a yakin neman zabe?
Hauwa El-Yakub: Ba zan iya cewa ga dalili ba, tunda ni ba na yi. Domin ni ko kara ba na dauka a yawon neman zabe. Sai dai masu yi ba za su rasa nasaba da yin barazana ga abokan adawa ba. Amma ba batun kariya ba kamar yadda suke ikirari. Kuma a hakan muna shiga ko’ina a mazabun wannan yanki. Irin wadannan mutane ne ke lalata rayuwar ’ya’yan talakawa inda suke ba su makamai da miyagun kwayoyi don su yi musu abin da suke so. Muna kalubalantar irin wadannan mutane cewa ba mu taba ganin ’ya’yansu a harkar ba. Idan abu me kyau suke sa ’ya’yan mutane to su fito da nasu ’ya’yan. Aminiya: Wane kalubale mata ke fuskanta wajen fitowarsu takara?
Hauwa El-Yakub: Kalubalen da mata ke fuskanta bai wuce na rashin karbuwa a wurin jama’a ba inda ake ganin bai kamata mata su yi shugabanci ba. Sa dai a wannan karo wannan matsala ta kau domin a Kano a wannan karo malamai sun ba mu goyon baya sun bayyana cewa mace za ta iya wakilci.
Sai dai a yanzu ’yan siyasar da ba su da mulki a hannun wadanda ya hada maza da mata su ne ke fuskantar matsala daga wurin masu mulki, domin a wasu wurare ko fosta ba mu iya likawa. Akwai wani lokaci da na je wani wuri dan sanda ne ma ya hana mu lika fosta, ya ce idan mun lika sai mun gane kuskurenmu. Haka muka hakura saboda ya yi amfani da karfin mulki a kanmu.
Sai dai mun yarda cewa wannan fitowa da muka yi muna yi ne don gyara don haka babu gudu babu ja da baya har sai mun ga an tabbatar da gyaran ko da ba mu za mu yi gyaran ba .