Za a iya warware matsalar PDP cikin wata daya idan… -Alhaji Shehu Musa Gabam

Alhaji Shehu Musa Gabom wani jigo ne a jam’iyyar PDP. Shi ne tsohon Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Jihar Bauchi. A tattaunawar da ya yi da wakilinmu, ya bayyana dalilan rikice-rikicen PDP da kuma yadda za a magance su. Haka kuma ya yi hasashen yadda zabe zai kasance a 2015, kamar kuma yadda ya yi bayani […]

Za a iya warware matsalar PDP cikin wata daya idan… -Alhaji Shehu Musa Gabam

Alhaji Shehu Musa GabamAlhaji Shehu Musa Gabom wani jigo ne a jam’iyyar PDP. Shi ne tsohon Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Jihar Bauchi. A tattaunawar da ya yi da wakilinmu, ya bayyana dalilan rikice-rikicen PDP da kuma yadda za a magance su. Haka kuma ya yi hasashen yadda zabe zai kasance a 2015, kamar kuma yadda ya yi bayani kan dambarwar da ke faruwa tsakanin Shugaban kasa Goodluck Jonathan da wasu gwamnonin PDP na Arewa kan batun dawowar mulki Arewa. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

A matsayinka na jigo a jam’iyyar PDP, me za ka ce kan Rikice-rikicen da ke faruwa a wannan jam’iyya taku?
To, rikicin jam’iyyar PDP ba wani abu ne sabo ba a tarihin kafuwarta a Najeriya. Na farko, wadanda suka kafa wannan jam’iyya, mutane ne masu bambancin ra’ayoyi a siyasa amma suka zauna suka tatattauna, suka ga cewa ya dace don dawo mulkin siyasa a Nijeriya, bari su ajiye bambance-bambancen da ke tsakaninsu, su kafa wannan jam’iyya ta PDP.
Na san wadanda suka fara zama don kafa wannan jam’iyya, tun ana G7, wanda aka yi a gidan marigayi tsohon Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abubakar Rimi. A wannan lokaci ina cikin mataimakansa, na san da wannan zama na G7, har aka koma G18, har aka koma G34; har aka zo aka yi mata rijista.
Ganin yadda wannan rikici ya yi kamari, kana ganin za a iya warware shi kafin nan da zaben 2015?
Za a iya warware wannan rikici sai dai rikicin ya bambanta da sauran rikice-rikkicen da jam’iyyar ta taba fuskanta. Wannan rikici ya yi kamari, domin an samu matsala a shugabancin jam’iyyar. Wato shugabannin da suke shugabancin jam’iyyar na kasa na yanzu, ba su gano hanyoyin da za su warware shi ba.
Shugabannin jam’iyyar na baya sun kirkiro hanyoyin da suka kawo zaman lafiya a tsakanin ’ya’yan jam’iyyar. Na biyu kuma Shugaban kasa na yanzu da yake kan mulki, bai fahimci yadda harkokin siyasa suke ba. Don haka ya kasa zaunar da ’ya’yan jam’iyyar domin a warware wannan rikici.
Kuma aka zo aka sami matsaloli tsakanin Shugaban kasa da gwamnonin jihohi. Tuni muke gaya wa PDP cewa kada su damka wa gwamnoni shugabancin jam’iyya, domin matukar aka damka masu ita, aka ba su karfi, to ruwa mutum in zai sha a wannan jam’iyya; idan gwamnan jiharsa ba ya so, ba zai sami ruwan nan ba. Wannan mummunar illa ce ga kowace jam’iyya da siyasar ga baki daya. Ya kamata a ce jam’iyya ce gaba da kowa. Wannan shi ne ya kara wa jam’iyyar PDP matsalar da ake ganin kamar ba za a iya warware ta ba. Amma za a iya warware wannan matsala matukar aka sami shugaba wanda ya san luggar siyasa. A cikin wata daya za a iya warware wannan matsala.
Wasu suna zargin shugaban PDP, Alhaji Bamanga Tukur da cewa shi ne ya kawo wa jam’iyyar want ton rikici da take ciki, me za ka ce kan wannan zargi?
Dole ne a zargi Bamanga Tukur, domin shi ne shugaban jam’iyyar. Idan wannan jam’iyya ta yi kyau shi ne, idan wannan jam’iyya ba ta yi kyau ba shi ne. Ko matsalolin sun fi karfinsa mutane ba za su lura da haka ba, domin shi ne shugaban jam’iyyar. Don haka dole ya nemi hanyoyin da za a warware wannan matsala da jam’iyyar ta shiga. Idan bai nemi hanyoyin warware wannan rikici ba, ko ya sauka ko an sauke shi, za a ce shi ne ya kashe wannan jam’iyya. Wannan abu ba zai fita daga cikin tarihinsa ba. Saboda haka dole ne ya yi amfani da shekarunsa da kwarewarsa, ya tabbatar cewa wannan jam’iyya ta zauna lafiya.
Me za ka ce kan dambarwar da ake yi tsakanin Shugaban kasa da wasu gwamnonin PDP na Arewa kan maganar dawo da mulki Arewa?
Ni a wurina, wannan dambarwa da ake yi tsakanin Shugaban kasa da wasu gwamnonin PDP na Arewa kan maganar dawo da mulki Arewa, maganar banza ce. Domin na farko, ni ina cikin wadanda suka yi yaki kan mulki ya dawo Arewa a zaben da ya gabata na 2011. Ina cikin wadanda suka yaki Shugaban kasa Goodluck Jonathan kan mulki ya dawo Arewa kuma dukkan wadannan gwamnoni da suke wannan magana a yau, mun bi kansu mun yi masu magana  kan su goyi bayan mulki ya dawo Arewa. Domin a lokacin akwai fitattun ’yan Arewa da suka fito suna takara, kamar Janar Ibrahim Babangida da Alhaji Atiku Abubakar da Janar Aliyu Gusau a lokacin aka zo aka janye aka bar wa Atiku Abubakar. Amma wadannan gwamnoni da suke magana a yau suke cewa su ne ’yan Arewa masu kishin Arewa; suka ki zaben Atiku Abubakar, suka zabi Goodluck Jonathan. A yau ne kuma za su zo su ce suna kishin Arewa, don suna son wani ya zama Shugaban kasa a cikinsu. Duk abin da mutum ya yi ba don Allah ba zai gani. Wa suke son su yaudara?
Wato a ganinka, wannan yunkuri da wadannan gwamnoni suke yi na ganin mulki ya dawo Arewa, ba gaskiya ba ne?
Duk maganar banza ce, maganar son rai ce, maganar neman biyan bukatar kansu ce kawai, ba maganar Arewa ko kishinta suke yi ba. Suna daga cikin wadanda suka ci amanar Arewa.
Wane irin kalubale ne kake ganin sabuwar jam’iyyar nan ta APC za ta kawo wa wannan jam’iyya taku ta PDP?
Babu wani kalubale da wannan sabuwar jam’iyya ta APC za ta kawo wa PDP. Domin na farko duk jam’iyyar da aka yi ta sabuwa, kamar sabuwar amarya ce. Ana ganin ta da kyau, ana ganin ta da maiko amma idan aka huda ta, za a sami matsala. Saboda haka duk wani haba-haba da ake yi a kan wannan sabuwar jam’iyya, a ba su nan da watanni hudu zuwa biyar a ga yanayin tafiyarsu tukuna, ko za su iya hada kansu su fitar da mutum daya a cikinsu. Ai na PDP ake gani, a bari nasu ya fito tukuna.
Wanne hasashe ne kake da shi dangane da yadda zabubbukan 2015 za su kasance a kasar nan?
In Allah Ya yarda za a yi wadannan zabubbuka lafiya a Najeriya, domin idan ka san tarihin siyasar Najeriya, a duk lokacin da zabe ya kusa; babu irin abubuwan da ba a fada. Zaka ji ana cewa kasar za ta rushe, za a ce za a yi kaza-kaza da dai sauransu amma da zarar an fara yakin neman zabe, mutane suka samu abin yi, suna samun ’yan kudade; babu wanda zai damu ya je ya tayar da hankali. Don haka da zarar wadannan zabubbuka sun zo, za mu yi komai lafiya, za mu gama lafiya kuma za mu kafa mulki lafiya a 2015.

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50