Za a iya yin zaben kato bayan kato a Najeriya?

Lura da yadda zaben 2019 ke kara karatowa da yadda Jam’iyyar APC take shirin gudanar da zaben kato bayan kato a wasu daga cikin zabubbukan fid da gwaninta, wadansu sai suke tunanin cewa zai fi kamata a ajiye dukan na’ura kawai a yi zaben kato bayan kato a kirga, wanda ya fi mutane ya samu […]

Za a iya yin zaben kato bayan kato a Najeriya?
Za a iya yin zaben kato bayan kato a Najeriya?

Lura da yadda zaben 2019 ke kara karatowa da yadda Jam’iyyar APC take shirin gudanar da zaben kato bayan kato a wasu daga cikin zabubbukan fid da gwaninta, wadansu sai suke tunanin cewa zai fi kamata a ajiye dukan na’ura kawai a yi zaben kato bayan kato a kirga, wanda ya fi mutane ya samu nasara. A tunaninsu wannan ne kawai zai kawar da aringizon kuri’a. Sai dai wadansu suna tunanin ba zai yiwu ba saboda rashin tsaro. Hakan ya sa muka zagaya domin jin ra’ayoyin mutane, kuma ga amsoshinsu:

 

Ba zai yiwu ba a Najeriya – Halliru Ayuba

Umar Akilu Majeri, Dutse

Malam Halliru Ayuba Fagoji: “Zaben kato bayan kato ba zai yiwu ba yanzu a Najeriya domin zai jawo hatsaniya saboda ba a saba ba kuma zai haifar da gaba mara iyaka a tsakanin al’umma. Kamata ya yi a yi zaben jami’an jam’iyya amma a sirrince cikin daki. Amma kato bayan kato ba abin da zai jawo sai rigima da za a iya rasa rayuka.”

 

Ba abin da zai hana a gudanar da zaben – Abubakar Isa Sakkwato

Daga Nasiru Bello, Sakkwato

Abubakar Isa Sakkwato: “Ba abin da zai hana a gudanar da zaben kato bayan kato a Najeriya saboda duk wasu matsaloli da za a iya hangowa in an yi zaben gaskiya babu su. Don yanzu mutane suna zabar wadanda ba su sani ba a kauye, amma in zaben kato bayan kato ne fa duk wanda ka zaba ka san shi da amfaninsa. Wata hanya ce ta saukaka wa hukumar zabe gudanar da zabe cikin sauki da lumana, sabanin inda aka fito da za a yi zabe a yi sama-da-fadi da sakamakon zabeN. Zaben keke-da-keke zai kara sa duk wanda aka zaba ya rika dawowa ga mutanensa don ya san alkawarin da ya yi in bai cika ba ya san ido da ido za a sake haduwa. Ka ga dole kowa ya shiga taitayinsa. Ba Jam’iyar APC kadai ba, kamata ya yi hukumar zabe ta gudanar da irin zaben a Najeriya don cimma burin Shugaba Buhari na gudanar da zabe sahihi, a kasar nan.”

 

Zaben kato bayan kato zai yiwu a Najeriya – Hamisu Adamu

Daga Hussaini Isah, Jos

Malam Hamisu Adamu: “A fahimtata zaben kato bayan kato zai yiwu a Najeriya, matukar shugabanni da jam’iyyu  suka goyi bayan abin. Kuma matukar ana son a samu shugabanni nagari wadanda talakawa suke so, to wannan tsarin zaben na kato bayan kato ne mafita. Kuma wannan tsari zai bai wa talakawan da ake shugabanta dama su zabi shugabannin da suke so, ba wadanda za a dora musu ba. Don haka ni a ra’ayina zaben kato bayan kato zai yiwu a Najeriya.” 

 

Abu ne mai kyau – Inuwa Muhammed

Umar Akilu Majeri, Dutse

Malam Inuwa Muhammed Barangu: “Yin zaben kato bayan kato a Najeriya abu ne mai kyau kuma shi ne ya fi sauki saboda shi zabe ne da ba a bata lokaci saboda kidaya kawai ake yi, kuma shi babu maganar magudi, in ka ci, ka ci kawai, in kuma ba ka ci ba, ba kaci ba ne. Kuma yanzu yin zabe a shiga daki a dangwala ya zama tsohon yayi a wajen mutane. Sanin kowa ne babu inda ake yin magudin zabe kamar inda ake shiga daki a yi aringizon kuri’a, amma idan kato bayan kato ne za a yi maganin magudin zabe, duk wanda ya fadi ya san ya fadi.”

 

kato bayan kato zabe ne na adalci – Muhammad Aliyu Faruk

Daga Nasiru Bello, Sakkwato

Muhammad Aliyu Faruk: “Zai yiwu kuma yin sa ne zai nuna zaben za a yi adalci domin talaka zai zabi ra’ayinsa kuma wanda zai wakilce shi. Shugabanni a kasar nan suna tsoron zaben kato bayan kato, amma mu talakawa muna son a yi shi don mun san shi ne kadai hanyar da muke iya zaben wanda muke so sabanin yadda iyayen gidan siyasa ke dora mana wanda suka ga dama ko muna so ko ba mu so. Sai wadansu talakawa su rika sayar da ’yancinsu ga bara-gurbin ’yan siyasa. Da zaben kato bayan kato ake yi, da an dade da mantawa da sunan wadannan ’yan siyasa.

 

Zaben kato bayan kato ba zai yiwu a Najeriya ba – Auwalu Sharubutu

Daga Hussaini Isah, Jos

Auwalu Sharubutu: “Gaskiya a ra’ayina zaben kato bayan kato, ba zai yiwu a Najeriya ba, saboda irin halayenmu na ’yan Najeriya. Domin rigima za a yi a wasu wurare da dama, idan jam’iyyu suka ce za a yi zaben kato bayan kato. Don haka a ra’ayina jam’iyyu su yi zaben tsarin wakilai da aka saba. Domin shi ne zai magance rikice-rikice a wuraren zaben tsayar da ’yan takara. Amma idan aka ce za a yi zaben kato bayan kato to za a samu rikice-rikice. Don haka zaben kato bayan kato ba zai yiwu ba a Najeriya.”