Za a je zagaye na biyu na zaben Shugaban kasa a Tunusiya

Hukumar zabe a kasar Tunusiya ta ce za a je zagaye na biyu na zaben Shugaban kasa, bayan Shugaban kasar Moncef Marzouki ya sha kayi a hannun dan takarar da ba ruwansa da addini, Beji Caid Essebsi, ranar Lahadin da ta gabata. Mista Essebsi na jam’iyyar Nidaa Tounes ya samu kashi 39.46 cikin 100, Mista […]

Za a je zagaye na biyu na zaben Shugaban kasa a Tunusiya
Za a je zagaye na biyu na zaben Shugaban kasa a Tunusiya

Hukumar zabe a kasar Tunusiya ta ce za a je zagaye na biyu na zaben Shugaban kasa, bayan Shugaban kasar Moncef Marzouki ya sha kayi a hannun dan takarar da ba ruwansa da addini, Beji Caid Essebsi, ranar Lahadin da ta gabata.
Mista Essebsi na jam’iyyar Nidaa Tounes ya samu kashi 39.46 cikin 100, Mista Marzouki kuma ya samu 33.4 cikin 100 kamar yadda hukumar zaben kasar ta bayyana. Har ila yau, Essebsi mai shekara 87, ya taba aiki da hanbararriyar gwamnatin Zine el-Abidine Ben Ali, yayin da Marzouki mai shekara 69 yake samun goyon bayan masu bin addini sau-da-kafa.
Masana na ganin cewa za a fafata sosai a zagaye na biyu na zaben saboda bambanci da ke tsakanin ’yan takarar ba mai yawa ba ce. Kuma tuni mutanen biyu suka fara yakin neman zabe. Kafar talabijinn ta Aljazeera ta ruwaito cewa an bai wa duka ’yan takarar kwana uku don su gabatar da korafinsu. Idan kuma hukumar zaben ba ta samu wani koke ba, za ta zabi ranar 14 ko 21 ga watan gobe a matsayin ranar gudanar da zagaye na biyu na zaben. Amma idan aka samu wani korafi daga akalla daya daga cikin’yan takarar, to za a gudanar da zaben ne a ranar 28 ga watan goben.
Hakazalika, a ranar Talatar da ta gabata ne shugaban Hukumar Tarayyar Turai , daya daga cikin wadanda suka sanya ido a zaben suka bayyana cewa an gudanar da zaben na farko a kasar tun bayan juyin juya-halin shekarar 2011 cikin adalci da gaskiya.
dan takarar da zo na uku Hamma Hammami na jam’iyyar Tunisia’s Popular Front ya samu kashi bakwai ne cikin dari na kuri’un da aka kada. Kuma jam’iyyar masu bin addini sau-da-kafa ta Ennahda  ba ta gabatar da kowane dan takara ba a zaben, amma an yi amannar cewa magoya bayanta  suna goyon bayan shugaba mai ci ne.