Za a kaddamar da littafin tarihin M. D. Yusuf

Shirye-shirye sun kankama na kaddamar da littafin tarihin rayuwar tsohon Sufeto-Janar na ’Yan sanda, M. D. Yusuf.Littafin, mai taken ‘Nagarta Cikin Aminci,’ wanda Abubakar Ado Mijinyawa ya rubuta, za a kaddamar da shi ne a ranar 18 ga watan jibi a Gidan Tarihi na Arewa da ke Kaduna.Kwamitin kaddamarwar, wanda ke karkashin shugabancin tsohon Sufeto-Janar […]

Za a kaddamar da littafin tarihin M. D. Yusuf

Shirye-shirye sun kankama na kaddamar da littafin tarihin rayuwar tsohon Sufeto-Janar na ’Yan sanda, M. D. Yusuf.
Littafin, mai taken ‘Nagarta Cikin Aminci,’ wanda Abubakar Ado Mijinyawa ya rubuta, za a kaddamar da shi ne a ranar 18 ga watan jibi a Gidan Tarihi na Arewa da ke Kaduna.
Kwamitin kaddamarwar, wanda ke karkashin shugabancin tsohon Sufeto-Janar kuma Sardaunan Katsina, Alhaji Ibrahim Coomassie, ya bayyana a cikin wata takardar da aka raba wa manema labarai cewa; za a yi gidauniyar tara kudi a wurin kaddamar da littafin, inda za a yi amfani da su wajen gina katafariyar cibiyar bincike da bunkasa ilimi a Jihar Katsina.
Kamar yadda sakataren kwamitin kaddamarwar, Malam danjuma Katsina ya shaida wa Aminiya, ya ce ba wannan ne littafi na farko da aka taba wallafawa game da tarihin rayuwar Alhaji M. D. Yusuf ba, amma dai shi ne irinsa na farko da aka wallafa da Hausa game da shi. Ya kara da cewa ko a shekarun baya, an wallafa littattafai biyu da Ingilishi, masu taken: ‘Beyond the Cop’ da kuma ‘The Aristocratic Rebel.’

Zanga-zanga ba za ta hana mu rusau a Abuja ba — Wike 

Lakurawa: Muna buƙatar taimakon Sakkwatawa — Hafsan Sojin Ƙasa

Mayakan Lukurawa sun kashe mutum 17 a Kebbi

Tsadar kayan abinci da rashin tsaro a Arewa abun damuwa ne —Sanata Babangida