Za a kafa kasuwannin hada-hadar gwala-gwalai a Kano da Legas

Gwamnatin tarayya ta ce za ta kafa kasuwannin cinikin gwala-gwalai a jihohin Kano da Legas domin hada-hadar wadanda aka hako a gida Najeriya. Ministan Karafa, Olamilekan Adegbite shine ya bayyana hakan a Abeokuta babban birnin jihar Ogun yayin wani baje-kolin kan hanya da ma’aikatarsa ta shirya a jihar a karshen mako. EFCC ta kwace gwala-gwaln […]

Za a kafa kasuwannin hada-hadar gwala-gwalai a Kano da Legas

Wata kasuwar gwala-gwalai

Gwamnatin tarayya ta ce za ta kafa kasuwannin cinikin gwala-gwalai a jihohin Kano da Legas domin hada-hadar wadanda aka hako a gida Najeriya.

Ministan Karafa, Olamilekan Adegbite shine ya bayyana hakan a Abeokuta babban birnin jihar Ogun yayin wani baje-kolin kan hanya da ma’aikatarsa ta shirya a jihar a karshen mako.

Ya ce za a bullo da shirin ne da nufin fadada hanyoyin samar da kudaden shiga a kasa daga hanyoyin da ba na man fetur da iskar gas ba.

A cewarsa, “Za mu gina sabbin kasuwannin a Kano da Legas inda mutane daga kowanne sashe na duniya za su iya zuwa domin sayen kayan kawa na gwala-gwalai.

“Wannan zai taimaka sosai wajen kara samar da ayyukan yi ga al’umma da kuma bunkasa hanyoyin kudaden shigar gwamnati,” inji shi.

Ya kuma lura cewa yinkurin gwamnatin na fadada hanyoyin habaka tattalin arziki ne ya zaburar da ita kan fadawa harkar hakowa da kuma sarrafa gwala-gwalai a jihar Kano ka’in da na’in domin habaka tattalin arzikin kasa.

Ya ce Najeriya ta sami gagarumar nasara a kan harkar musamman a jihar Kano a kwana-kwanan nan, yana mai cewa da wannan sabon shirin nasu, kasar na dab da shiga sahun kasashen da ke kan gaba a harkar a duniya.

Minista Olamilekun ya kuma ce Najeriya za ta hada gwiwa da gwamnatin kasar Jamus domin horar da ‘yan kasarta 45 a kan harkar hakowa da kuma sarrafa gwala-gwalan na tsawon watanni tara.