Za a kafa makarantar horar da ’yan sanda a Nasarawa

Za a kafa makarantar horar da ’yan sandan kwantar da tarzoma a mashigin dutse da ya fi kowane hadari a Jihar Nasarawa da aka fi sani da  “Mutane da yawa sun mutu.” Gwamnan Jihar Nasarawa, Alhaji Abdullahi Sule ne ya bayyana haka yayin da ya ziyarci ofishin Sufeto Janar na ’yan sandan Najeriya Mohammed Adamu […]

Za a kafa makarantar horar da ’yan sanda a Nasarawa

Shugaban ’Yan sandan Najeriya Mohammed Adamu

Za a kafa makarantar horar da ’yan sandan kwantar da tarzoma a mashigin dutse da ya fi kowane hadari a Jihar Nasarawa da aka fi sani da  “Mutane da yawa sun mutu.”

Gwamnan Jihar Nasarawa, Alhaji Abdullahi Sule ne ya bayyana haka yayin da ya ziyarci ofishin Sufeto Janar na ’yan sandan Najeriya Mohammed Adamu don gode masa kan kafa makarantar a mashigin da ya shahara wajen mummunan ayyuka da suka hada da fashi da garkuwa da mutane da haddura.

Mashigin da ke garin Endehu yana cikin Karamar Hukumar Nasarawa Eggon ne.

Rahotanni sun ce makaranar ta horar da ’yan sandan ita ce irinta ta uku a kasar nan, kuma ta kunshi hecta 180.

Gwamnan ya samu rakiyar Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Aliyu Tijjani Ahmed da sauran manyan mutane.

A jawabin Sufeto Janar Mohammed Adamu ya ce ba za su yi kasa a gwiwa ba domin ganin an samu zaman lafiya a kasar nan.

Shugakban Karamar Hukumar Nasarawa Eggon, Danlami Idris Odasko ya ce suna murna da kafar makarantar, kuma yin hakan ya dace kwarai don za a samu karin tsaro a mashigin.

Idan ba a manta ba, a wajen ne Mataimakin Gwamman Jihar Nasarawa Dokta Samuel Akabe ya tsallake rijiya da baya a wani lokaci a baya, inda aka kashe ’yan sanda hudu da ke tare shi.