Za a kafa rundunar yaki da Boko Haram
Shugabannin kungiyar kasashen Bakin Tafkin Chadi (LCBC) sun amince su kafa wata rundunar soja ta hadin gwiwa domin yaki da kungiyar Boko Haram.A wani taro da suka gudanar a Jamhuriyyar Nijar a ranar Talata da ta gabata, shugabannin da suka hada da Goodluck Jonathan na Najeriya da ta fi fama da hare-haren Boko Haram da […]
Shugabannin kungiyar kasashen Bakin Tafkin Chadi (LCBC) sun amince su kafa wata rundunar soja ta hadin gwiwa domin yaki da kungiyar Boko Haram.
A wani taro da suka gudanar a Jamhuriyyar Nijar a ranar Talata da ta gabata, shugabannin da suka hada da Goodluck Jonathan na Najeriya da ta fi fama da hare-haren Boko Haram da Paul Biya na Kamaru da kasarsa ke fuskantar barazanar kungiyar da Idris Derby na Chadi da kuma Mohamoudu Yousouf na Nijar sun amince da haka ne a taron da suka gudanar a birnin Yamai na kasar Nijar domin nazari kan matsalolin tsaron da ake fuskanta a yankin na tafkin Chadi.
A karkashin tsarin, kowace kasa za ta tura sojojinta kan iyakokinta da tafkin Chadi.
Kuma a wata hira da gidan rediyon BBC, Ministan Harkokin Wajen Nijar, Malam Bazoum Muhammed ya ce a yanzu kasar Kamaru ta amince ta ba da cikakken hadin kai, bayan zargin da aka rika yi mata a baya cewa, tana jan kafa a wajen daukar matakan yaki da kungiyar Boko Haram.
A farkon wannan mako ne wani sabon rahoto ya ce akalla mutanen da aka hallaka a sanadin ta’asar ’yan Boko Haram a sashin Arewa maso Gabas na kasar nan sun kai mutum dubu 11.
Wannan adadi ya fito ne a cikin wani nazarin da Sashin Nazarin Al’amurran Yau da Kullum na Duniya a Jami’ar John Hopkins da ke kasar Amurka ya gudanar bayan da ya hada jimillar mutanen dake rasu tun daga lokacin da aka faro tashin hankalin a shekarar 2009.
Rahoton wanda aka wallafa a jaridar Washington Post ta Amurka, masu nazarin sun ce yanzu a duniya ba wata tarzoma da kai ta Boko Haram ta fuskar asarar rayukan mutane. Rahoton ya ce a cikin shekara daya kawai, daga watan Yulin 2013 zuwa watan Yunin bana, mutanen da aka kashe a tarzomar Boko Haram sun fi mutum dubu bakwai, wanda hakan ya nuna mutanen da ake kashe a yake-yaken Iraki da Afghanistan ba su kai yawan wadanda aka hallaka a hannun ’yan Boko Haram da ma’aikatan tsaron kasar nan ba, wadanda su ma rahoton ya ce ana zarginsu da yi wa dimbin mutane kisan gilla da suna yaki da ’yan Boko Haram.
Rahoton ya ce in aka yi jimillar ’yan Najeriya da suka rasu a tashe-tashen hankula masu alaka da addini da kabilanci da siyasa da tattalin arziki daga 1998 zuwa yau, sun fi mutum dubu 30.