Za a kai shugaban ’yan sanda kotu kan kudin otel N625m

Tawagar SWAT sun mamaye bababn otal din mai dakuna 50, inda suka mayar da shi sansaninsu ba tare da izini daga masu shi ba.

Za a kai shugaban ’yan sanda kotu kan kudin otel N625m

Shugaban ‘yan sandan Najeriya

Mallakin wani babban otel a Jihar Bayelsa ya yi barazanar kai Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Kayode Egbetokun Kotu, a kan zargin bashin miliyan N625m da yake bin rundunar ’yan sanda ta SWAT.

Tawagar SWAT da aka tura yankin Opu Nembe domin wanzar da zaman lafiya gabanin zaben gwamnan jihar da ya gabata sun tare a shahararren otel din Euphemie Motel da ke yankin tun ranar 12 ga Agusta, 2023 har zuwa yau.

Ana zargin a yayin wani samame a yankin ne tawagar, karkashin wani CSP Silas Adebayo, suka mamaye otal din, inda suka mayar da shi sansaninsu ba tare da izini daga masu shi ba.

Lauyansa, Inemoye Maxwell Brown Esq., a wasikarsa ga shugaban rundunar, Kayode Egbetokun da shugaban hukumar ’yan sanda, ya ce kudin duk daki a otal din mai dakuna 50 Naira 25,000 ne a kullum, akwai kuma taro guda biyu kowanne a kan N100,000 a kowace rana.

Sanann akwai wuraren shakatawa na waje, a mma duk jami’an rundunar sun mamaye su ba tare da biya ba, sama da watanni 13.

“Harkokin kasuwancin sun rushe kuma babu makawa sai an yi gyara sannan ya zama wajibi a maido da kayan aikinsu domin su ci gaba da harkokinsu na yau da kullum.

“Muna kira ga shugaban ’yan sanda ya umurci jami’anku da suka shiga otal din da karfin tsiya daga ranar 12 ga watan Agusta, 2023 zuwa yau, cewa su fice nan da makonni shida bayan samun wannan wasika.

“Za kuma a biya N625,000,000 na lokacin da suka mamaye ginin a cikin makonni shida bayan karbar wasikar nan,” a cewar Inemoye Maxwell Brown Esq.

A cewarsa, idan aka buris da wasikar, “za mu tunkari kotu don neman diyya ga dukiyar wanda ake tuhuma.”

Da aka tuntubi kakakin rundunar a jihar Bayelsa, ASP Musa Muhammed, ya ce a ba zai iya cewa magana ba saboda rashin kyan hanyar sadarwa a inda yake, amma da wakilinmu ya kira shi daga bisani bai amsa kiran ba.

Hatsarin kwalekwale ya ci rayuka 4 a Borno

Lokacin Soke Tallafin Mai A Najeriya Ya Yi —Dangote

Gwamnatin sojin Burkina Faso ta ce ta sha daƙile yunƙurin hargitsa ƙasar

Za a kai shugaban ’yan sanda kotu kan kudin otel N625m