Za a kai shuganban Hukumar KANUPDA kotu kan rushe masallaci

Iyalan marigayi Alhaji Nasidi Usama sun yi barazanar kai shugaban Hukumar Tsara Birane ta Jihar Kano (KANUPDA) Alhaji Isyaku Muktari Kura kotu, bisa rushe farin masallaci da ke kan titin Zariya a Unguwar Gyadi-Gyadi a karamar Hukumar Tarauni cikin birnin Kano. Aminiya ta gano cewa an rushe masallacin ne a ranar Juma’ar da ta gabata […]

Za a kai shuganban Hukumar KANUPDA kotu kan rushe masallaci
Za a kai shuganban Hukumar KANUPDA kotu kan rushe masallaci

Iyalan marigayi Alhaji Nasidi Usama sun yi barazanar kai shugaban Hukumar Tsara Birane ta Jihar Kano (KANUPDA) Alhaji Isyaku Muktari Kura kotu, bisa rushe farin masallaci da ke kan titin Zariya a Unguwar Gyadi-Gyadi a karamar Hukumar Tarauni cikin birnin Kano.

Aminiya ta gano cewa an rushe masallacin ne a ranar Juma’ar da ta gabata da misalin karfe 10 na safe, kuma wasu daga cikin ’ya’yan marigayin da suka hada da Mustapha da
Suraj Nasidi Usama sun shaida wa Aminiya cewa mahaifinsu ne ya gina masallacin shekaru 24 da suka gabata da yardar gwamnatin Jihar Kano.
Sun ce kimanin wata uku da suka gabata hukumar ta shafa jan fenti a jikin katangar masallacin inda ta rushe katangar tare da biyan diyyar Naira miliyan biyu da dubu 200.
“Bayan ’yan kwanaki da yin hakan sai kuma ga motar kamfanin TEC ta zo kofar masallacin da niyyar rushe shi gaba daya a nan muka tambaye su dalilin yin hakan sai suka ce MD din KANUPDA ne ya bayar da umarnin hakan. Babu irin rokon da ba mu yi musu ba amma suka ki saurarenmu sai da suka aiwatar da abin da ya kawo su. Hakan ya sa muka dauki matakin shari’a da shi kadai, domin labari ya iske mu cewa Gwamnan Jihar Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso bai ji dadin rushe masallacin ba,” inji su.
Har ila yau ‘ya’yan marigayin sun ce wata majiya mai tushe ta shaida musu cewa shugaban ya yi barazanar rushe gidansu matukar ba su daina shiga kafafen watsa labarai suna wannan magana ba.
Yayin da Aminiya ta tuntubi Shugaban Hukumar KANUPDA Alhaji Isyaku Muktari Kura ya karyata abin da suka fadi inda ya ce masu wannan da’awa ba su da takardar shaidar mallakar filin gaba daya. “Ba ma tsoron su kai maganar kotu. Mun gode wa Allah da suka gaya muku cewa an biya su diyya, sai dai suna cewa kudin ne bai isa ba, don haka muka shaida musu cewa su kai korafinsu ga Kwamishinan kasa da Safiyo,” injin shi.

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya

Gwamnatin Tinubu na yunƙurin hana ni yin takara — Peter Obi

An gurfanar da ƙarin mutum 17 bisa zarginsu a kisan malama

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi