Za a kara aurar da zawarawa 2000 a Kano

Hukumar Hisba ta Jihar Kano ta bayyana cewa tana nan tana shirye-shiryen sake gudanar da auren zawarawa a karo na hudu a jihar. Da yake wa Aminiya karin haske, Darakta Janar na Hukumar Hisba Dokta Abba Sufi, ya bayyana cewa hukumarsu za ta gudanar da wannan aure ne a farkon shekara mai kamawa, kamar yadda […]

Za a kara aurar da zawarawa 2000 a Kano
Za a kara aurar da zawarawa 2000 a Kano

Hukumar Hisba ta Jihar Kano ta bayyana cewa tana nan tana shirye-shiryen sake gudanar da auren zawarawa a karo na hudu a jihar.

Da yake wa Aminiya karin haske, Darakta Janar na Hukumar Hisba Dokta Abba Sufi, ya bayyana cewa hukumarsu za ta gudanar da wannan aure ne a farkon shekara mai kamawa, kamar yadda gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abdulalhi Umar Ganduje ta umarce su. “Mun samu wannan umarni ne daga Gwamna Abdulalahi Umar Ganduje cewa mu shirya gudanar da auren zawarawa kimanin 2000 wanda ake sa rai za a yi shi zuwa farkon shekara mai kamawa.” Inji shi.
Dokta Sufi ya bayyana cewa, “Za mu fito da sabbin tsare-tsare don ganin an yi maganin ire-iren matsalolin da aka ci karo da su a baya. Zan yi amfani da wannan dama wajen yin kira ga ma’auratan da za su ci moriyar shirin da su bai wa hukumarmu hadin kai don ganin an samu nasarar shirin gaba daya.” Inji shi
Tunda farko Darakta Janar din ya bayyana cewa manufar gwamnati na bullo da wannan shiri na auren zawarawa bai wuce kokarin da gwamnatin ke yi wajen magance matsalar karuwanci da kuma sauran abubuwa na badala a tsakanin al’umar jihar ba, wanda kuma gwamnatin ta ci alwashin ganin dorewar shirin.
Shi ma da yake karin haske game da shirin na auren zawarawan, Kwamanda Janar na hukumar Hisba Ustaz Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana cewa hukumarsu tana da kwamitin mata wanda ke bibiyar halin zamantakewar da ma’auratan da hukumar ta aurar suke ciki. “Musamamn muka kafa kwamitin mata da ke bibiyar halin da ma’auratan ke ciki. A halin yanzu labari masu dadi yana zuwar mana daga gidajen ma’aurata dubu biyar da muka aurar, sai dan kadan da ba a rasa ba. Alhamdulillah ma’aratan suna zaune lafiya da junansu, har sun haifi yaya masu yawa.” Inji Daurawa
Idan dai za a iya tunawa, kimanin zawarawa dubu biyar ne suka ci moriyar shirin auren zawarawa, shirin da gwamnatin jihar karkashin jagorancin tsohon Gwamna Injiniya Rabiu Musa kwankwaso ta bullo da shi a shekarar 2012.
A wani ci gaban kuma Gwamantin Jihar Kano ta nada Shaikh Shehi Ibrahim Maihula a matsayin sabon Shugaban Hukumar Hisba.
Da yake jawabi a lokacin tarbar sabon Shugaban Hisbar, Kwamandan Janar na Hisba Ustaz Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana cewa shigar jami’an Hisba cikin harkokin siyasa ita ce babbar matsalar da hukumar ke fama da ita.
Daurawa ya kara da cewa, a yanzu haka Hukumar Hisba tana da ma’aikata dubu 10, wanda dubu uku daga ciki mata ne, a cikin birni da kananan hukumomin jihar 44.
Har ila yau Ustaz Daurawa ya bayyana cewa, a yanzu haka shirye-shirye sun yi nisa na bude makarantar Hisba, inda jami’anta da kuma duk wani da ke son yin aiki a hukumar za su rika samun horo na musamamn a kan sha’anin aikin hukumar.
Shi ma a nasa jawabin sabon Shugaban Hisbar Shaikh Shaikh Ibrahim Maihula, ya yi alkawarin tafiyar da ayyukan hukumar cikin gaskiya da adalci ba tare da nuna bambanci ba , inda ya yi kira ga masu ruwa da tsaki a hukumar da su ba shi hadin kai wajen ciyar da hukumar Hisba gaba.