Za a karrama daraktan fina-finan Koriya ta kudu
Daraktan fina-finan nan dan kasar Koriya ta kudu, Im Kwon-teak, wanda ya lashe gasar fasahar fina-finai ta Cannes ya kara samun daukaka, inda a bana za a karrama shi da wata babbar kyauta a yayin bikin karrama ’yan fim mai taken Singapore International Film Festibal, wanda shi ne karo na 25 da za a gudanar […]
Daraktan fina-finan nan dan kasar Koriya ta kudu, Im Kwon-teak, wanda ya lashe gasar fasahar fina-finai ta Cannes ya kara samun daukaka, inda a bana za a karrama shi da wata babbar kyauta a yayin bikin karrama ’yan fim mai taken Singapore International Film Festibal, wanda shi ne karo na 25 da za a gudanar a watan Disamba mai zuwa.
Daraktan, dan shekara 78 da haihuwa, zai amshi kambin karramawar ne saboda la’akari da irin gudunmowar da ya ba da wajen bunkasa harkar fim a duniya. Bikin zai gudana ne a ranar 13 ga watan Disamba mai zuwa. Kasancewar bikin na kwanaki uku ne, za a kuma nuna wasu daga cikin fina-finansa da suka hada da Mandara (1981), billage of Haze (1982) da kuma Rebibre (2014), wanda shi ne fim dinsa na 102 da aka nuna a birnin benice.