Za a karrama manyan marubuta da malaman Hausa na Najeriya da Nijar
kungiyar Marubuta Harsunan Gida Ta Nijar (ASAUNIL) tare da hadin gwiwar takwararta ta Najeriya (NILWA) sun shirya gagarumin taron kara wa juna sani na kwana uku a birinin Yamai, Jamhuriyar Nijar domin tunawa da kuma karrama fitaccen malamin Hausa, marigayi Farfesa Hambali Junju.Taron wanda za a gudanar daga ranakun 18 zuwa 21 ga watan nan, […]
kungiyar Marubuta Harsunan Gida Ta Nijar (ASAUNIL) tare da hadin gwiwar takwararta ta Najeriya (NILWA) sun shirya gagarumin taron kara wa juna sani na kwana uku a birinin Yamai, Jamhuriyar Nijar domin tunawa da kuma karrama fitaccen malamin Hausa, marigayi Farfesa Hambali Junju.
Taron wanda za a gudanar daga ranakun 18 zuwa 21 ga watan nan, za a gabatar da shi ne a zauren taro na Emir Sultan benue da ke Yamai, Babban Birnin Jamhuriyar Nijar. Taken taron dai shi ne: ‘kalubalen Da Ke Tattare Da Koyar Da Yarukan Afrika.’
A wata tattaunawa da daya daga cikin jami’o’in gudanarwar na kungiyar Marubuta Harsunan Gida Ta Najeriya, Malam Ado Ahmad Gidan Dabino, ya bayyana wa Aminiya yadda tsarin taron zai kasance, inda a ranar farko da za a bude shi, za a gabatar da manyan baki, kafin daga bisani Gwamnan Yamai zai gabatar da jawabin maraba ga mahalarta taron. Daga nan ne kuma Shugaban kungiyar Marubuta Harsunan Gida Ta Nijar zai gabatar da nasa jawabin, sannan kuma takwaransa na Najeriya shi ma ya gabatar da nasa.
A ci gaba da taron, Ministan Ilimi na kasar Nijar zai gabatar da takaitaccen jawabi. Yana gamawa kuma sai Shugaban Jami’ar Bayero Kano shi ma zai gabatar da nasa takaitaccen jawabin. Haka shi ma Ministan Al’adun Gargajiya na kasar Nijar, zai gabatar da nasa jawabin.
Duk dai a wannan rana ta farko, taron zai ci gaba, inda mawallafin littattafai a Yamai, Mista Tarno Balla zai gabatar da takardarsa, inda bayan ya kammala, shi ma Shugaban Tsangayar Harsuna ta Jami’ar Bayero Kano, Malam Muntari Yusif zai gabatar da tasa takardar. Za a dan tsahirta na dan lokaci domin hutu, kafin daga nan kuma a dawo domin tattauna takardun da malaman suka gabatar.
Ba takardu kawai za a gabatar a ranar farko ba, domin kuwa da dare, mahalarta taron za su halarci kasaitaccen biki, inda makada da mawakan gargajiya za su taya su hira da wakokinsu da kade-kadensu, kamar kuma yadda za a gabatar da wasannin kwaikwayo na dabe.
A rana ta biyu ma, za a gabatar da malamai daban-daban, wadanda za su gabatar da takardu daban-daban, daga bisani kuma a tattauna a kansu. A kuma ranar ce Farfesa Ado Mahamane na Jami’ar Abdou Moumouni zai gabatar da tasa takardar. Da dare kuwa, nan ma mahalarta taron za su samu nishadantarwa daga marubutan labarun kirkira, inda za su yi karance-karancen kirkirarrun labarunsu da kuma wakokin fasaha. Masu gabatar da wasannin kwaikwayo ma ba za a bar su a baya ba.
A rana ta uku kuma ta karshe, wato 21 ga wata, rana ce da za ta kasance ta rufe taron. A wannan rana ce za a bayyana takardar bayan taro sannan kuma a karrama wasu daga cikin fitattun malamai da marubuta da shugabannin al’umma da suka fito daga kasashen Najeriya da Nijar.
A wata takarda da Aminiya ta samu, wacce Sakataren shirya taron Mista Aboubacar Mahamane ya sanya wa hannu, an bayyana sunayen wadanda za a karrama a wajen taron, kamar haka:
Daga kasar Nijar, wadanda za a karrama sun hada da, Shugaban kasar Nijar Muhammadou Issofou da tsohon Shugaban kasar Nijar, Muhammadu Tandja da Ministan Sadarwa na Nijar da Ministan Ilimi na Nijar da Ministan Al’adun Gargajiya na Nijar da Babban Darakta na Hukumar Tarihi ta CELTO.
Sauran sun hada da Mista Thomas B. da ’yar jarida Lidiya Ado da Maliki Alasan da kuma gidan rediyo mai zaman kansa, wato Radio Al’umma.
Daga Najeriya kuwa, wadanda za a karrama sun hada da Mai martaba Sarkin Daura, Alhaji Farouk Umar Farouk, a matsayinsa na mai kula da kare martabar Hausa da Hausawa. Akwai kuma tsohon Sufeto-Janar Alhaji Ibrahim Commassie, a matsayinsa na Garkuwan Hausa kuma mai yi wa Hausa hidima. Sai Sadiya Ado Bayaro, Giwar danmaje, wacce ta taimaka wajen tattarawa da wallafa ire-iren kirarin da ake samu a masarautun kasar Hausa.
Sauran daga Najeriya sun hada da Farfesa Abdallah Uba Adamu, saboda kokarinsa na samar da haruffan Hausa a kwamfuta. Akwai Farfesa Ibrahim Malumfashi, saboda kwarewarsa da hidimarsa a fannin tarihin Adabi da rubuce-rubucen Hausa. Shi kuwa Dokta Bukar Usman, za a karrama shi ne a matsayinsa na marubucin da ya jajirce wajen farfado da tatsuniyoyi, hikaya da almara a kasar Hausa. Sai kuma mawakin zamani na Hausa, Aminuddeen Ladan Abubakar (ALA).
Akwai kuma fitattun malaman Hausa da suka mutu, wadanda kuma za a karrama a yayin gagarumin taron. Wadannnan mutane kuwa su ne marigayi Farfesa Hambali Junju, wanda ya kware wajen koyarwa da nazarin Nahawun Hausa. Sai kuma marigayi Farfesa Ibrahim Yaro Yahya, wanda shi kuma ya kware wajen nazari da koyar da Adabin Gargajiya na Hausa.
Kamar yadda Ado Ahmad Gidan Dabino ya shaida wa Aminiya, marubuta da masana da sauran al’umma da ke kishin harshen Hausa da sauran harsunan gida ne za su halarci gagarumin taron daga Najeriya da Nijar da sauran kasashen Afrika da sauran sassan duniya.