Za A Karrama Yara Marubuta a Bikin Littattafai na Akada a Legas

ACBF bikin baje kolin litattafan yaran Afirka ne, musamman Najeriya, da kuma wadanda aka rubuta don yara daga ko’ina a duniya.

Za A Karrama Yara Marubuta a Bikin Littattafai na Akada a Legas

Bikin littafan yara na farko kuma mafi girma a Najeriya, mai lakabin Akada Children’s Book Festival (ACBF), ya shirya gudanar da bikin karo na hudu a Jihar Legas.

Marubuciya kuma wacce ta assasa bikin, Oluwabunmi Abodunrin Talabi, ce ta bayyana hakan a ganawarta da manema labarai.

A cewarta, sabanin na shekarun 2021 da 2020 da aka gudanar ta yanar gizo sanadiyar COVID-19, bikin na bana a fili za a yi shi.

Ta ce za a yi shi ne ranar Asabar, 29 ga watan Oktoba, inda za a karrama yara 24 marubuta daga sassan Najeriya daban-daban.

“ACBF bikin baje kolin litattafan yaran Afirka ne, musamman Najeriya, da kuma wadanda aka rubuta don yara daga ko’ina a duniya.

“An kuma fara shi ne a shekarar 2019, kuma a lokacin mun yi tunanin mutane 400 ne za su halarta, amma sai muka samu 1,400”, in ji ta.

Kungiyar dai ta shirya bai wa yaran da suka samu nasara kyaututtuka, in da wanda ya zama na daya a fannin Rubutu da zane-zane, zai lashe kyautar Naira 100,000.