Za a kashe N3bn wajen kwaso ’yan Najeriya da suka mukale a Ukraine

Karamin Ministan Harkokin Waje Zubairu Dada ya fada cewa za a tura jirage uku don gudanar da aikin.

Za a kashe N3bn wajen kwaso ’yan Najeriya da suka mukale a Ukraine

Karamin Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Ambasada Zubairu Dada

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da kashe dala miliyan takwas da rabi – fiye da naira biliyan uku kenan – wajen aikin kwaso ‘yan kasar daga kasashe hudu makotan Ukraine sakamakon yakin da ake yi a can.

Ma’aikatar Harkokin Waje da hadin gwiwar ta agaji ne za su gudanar da aikin kwaso ‘yan kasar kusan 5,000 daga kasashen Poland da Ramania da Slovakia da Hungary.

Karamin Ministan Harkokin Waje Zubairu Dada ya fada wa manema labarai a ranar Laraba jim kadan bayan kammala taron Majalisar Zartarwa cewa za a tura jirage uku don gudanar da aikin jigilar.

Jiragen da za su yi jigilar sun kunshi na kamfanin Air Peace biyu da kuma na Max Air daya.

Wata sanarwa daga Ma’aikatar Harkokin wajen ta ce za a fara gudanar da aikin debo su bayan sun tsallaka makota daga Ukraine sakamakon fafatawar da ake yi tsakanin dakarun Rasha da na kasar.

Ta sanar a safiyar Laraba cewa, “Rukunin farko da za a kwaso za su iso Najeriya ranar Alhamis 3 ga watan Maris, 2022,” kuma kawo yanzu ofisoshin jakadancin Najeriya a kasashen hudu sun karbi ’yan Najeriya 2,090 a kan iyakokin kasar bayan sun tsallako daga Ukraine.