Za a kashe N61m wajen binne mutum 103 da aka kashe a zanga-zangar #EndSARS a Legas

A baya gwamnatin ta sha karyata cewa an kashe masu zanga-zangar

Za a kashe N61m wajen binne mutum 103 da aka kashe a zanga-zangar #EndSARS a Legas

Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu

Ana ci gaba da ce-ce-ku-ce bayan Gwamnatin Jihar Legas ta amince ta kashe Naira miliyan 61.2 domin binne mutum 103 da aka kashe yayin zanga-zangar #EndSARS a Jihar shekara uku da suka wuce.

A baya dai, gwamnatin Jihar da ma sojoji sun sha karyata rahoton kwamitin jin bahasin da aka kafa kan zanga-zangar, wanda ya ce jami’an tsaro sun bude wuta a kan masu zanga-zangar a Lekki Toll Gate ranar 20 ga watan Oktoban 2020.

An dai gudanar da zanga-zangar ce karshen shekara ta 2020, inda wadanda suka yi ta suka nemi a rushe sashen nan na Rundunar ’Yan Sanda mai yaki da ’yan fashi (SARS), saboda kaurin sunan da ya yi  wajen zargin take hakkin dan Adam.

Zanga-zangar dai, wacce a lokacin aka shafe tsawon makonni ana yin ta, da farko ta lumana ce, amma daga bisani ta rikide ta koma ta fasawa tare da sace kayayyaki a rumbunan gwamnati da na jama’a, kona ofisoshin ’yan sanda da kuma lalata dukiyoyi masu yawa.

To sai dai a wata wasika da idon Aminiya ya gani dauke da kwanan watan 19 ga watan Yulin 2023 ta Sashen Fitar da Kudade na gwamnatin Legas mai taken, “Jana’izar mutum 103 da suka mutu yayin zanga-zangar #EndSARS a 2020,” gwamnatin ta ce za ta yi aiki da wani kamfani mai suna Messrs Tos Funeral Ltd, inda za ta kashe Naira 61,285,000, wajen binne mutum 103.

Wasikar dai ta jawo ce-ce-ku-ce matuka, inda wasu masu fafutuka suke cewa hakan tamkar amincewa ne daga gwamnatin kan kisan mutanen, wanda a baya ta sha karyata cewa an kashe su.

To sai dai a wata sanarwa da Babban Sakataren Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Legas, Dokta Olusegun Ogboye, ya fitar da daren Lahadi, ya yi ikirarin cewa babu ko daya daga cikin gawarwaki 103 da aka kashe a Lekki Toll Gate.

Ya ce, “An tsinto su ne a unguwanni daban-daban sakamakon fada da aka yi a yankunan Fagba, Ketu, Ikorodu, Orile, Ajegunle, Abule-Egba, Ikeja, Ojota, Ekoro, Ogba, Isolo da Ajah na Jihar Legas.

“Kazalika, an fasa kurkukun Ikoyi. Mutum 103 da ake magana daga nan wuraren aka samo su, ba daga Lekki ba, sabanin yadda ake zargi,” in ji shi.

Babban Sakataren ya kuma ce za a yi jana’izar ce saboda an shafe shekara uku da faruwar lamarin, kuma gwamnatin ta ba da sanarwa ga dukkan iyalan wadanda suka rasa danginsu da su zo su duba gawarwakinsu, amma babu wanda ya je.

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025

Kirsimeti: Zulum ya ɗauki nauyin jigilar fasinjoji 710 zuwa garuruwansu

Ɗan shekara 60 ya rasu a hatsarin kwalekwale a Sakkwato

Yadda gobara ta ƙone kasuwar babura a Zamfara