Za a kashe Naira biliyan 1.5 a auren gata na mutum 1,500 a Kano — Hisbah

Za a kashe kusan Naira miliyan 1 kan kowanne ɗaya daga cikin ma’aurata domin samar musu kayayyakin fara rayuwar aure.

Za a kashe Naira biliyan 1.5 a auren gata na mutum 1,500 a Kano — Hisbah

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta sanar da cewa za a kashe kimanin Naira biliyan 1.5 a yayin auren gata na mutum 1,500 da gwamnatin jihar za ta gudanar.

Babban Kwamandan Hisbah na Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a ranar Litinin.

Sheikh Daurawa ya bayyana cewa daga cikin shirye-shiryen gudanar da auren gatan akwai gwaje-gwajen lafiya kafin aure, da suka haɗa da gwajin cutar HIV, ciwon hanta (Hepatitis), gwajin ciki da kuma gwajin ƙwayoyin halitta (Genotype), da sauransu.

Ya ce za a kashe kusan Naira miliyan 1 kan kowanne ɗaya daga cikin ma’aurata domin samar musu da kayayyakin gida, ciki har da gado, katifa, zanin gado, matasai, kayan ɗaki da kayan abinci.

A cewarsa, za a baiwa kowace amarya sadaki na Naira 100,000, sannan a ba ta ƙarin Naira 100,000 a matsayin jarin da za ta kama sana’a bayan aure.

“Auren gata na daga cikin alƙawuran da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi wa al’ummar Kano lokacin yaƙin neman zaɓe, kuma yanzu ya cika wannan alƙawari,” in ji Daurawa.

Kwamandan Hisbah ya kuma bayyana cewa hukumar ta sanar da masu shirin aure wata ƙa’ida da ke ƙarfafa musu nemi sasanci da Hukumar Hisbah kafin ɗaukar matakin rabuwa idan matsala ta taso a zamantakewarsu.

Haka kuma ya shawarci masu shirin aure da su tabbatar sun yi gwajin Genotype kafin aure domin kauce wa matsalolin da ke tattare da haihuwar yara masu fama da cutar sikila.

Daurawa ya ce za a sanar da ranar gudanar da auren gata da zarar Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da ranar da aka tsara.