Za a kashe Naira biliyan 10 wajen gina kananan hanyoyi a Jihar Adamawa
Bankin Duniya da Hukumar Bunkasa kasashe ta Faransa da hadin gwiwar Jihar Adamawa a karkashin Hukumar Gyara kananan Hanyoyi (RAMP), sun fara shimfida hanyoyi masu tsawon kilomita 341 da zai lashe Dala miliyan 50 (sama da Naira biliyan 10). Gwamnan Jihar Adamawa Muhammad Jibrilla Bindow ya ba da umarni shimfida hanyoyi masu nisan kilomita 201.4 […]
Bankin Duniya da Hukumar Bunkasa kasashe ta Faransa da hadin gwiwar Jihar Adamawa a karkashin Hukumar Gyara kananan Hanyoyi (RAMP), sun fara shimfida hanyoyi masu tsawon kilomita 341 da zai lashe Dala miliyan 50 (sama da Naira biliyan 10).
Gwamnan Jihar Adamawa Muhammad Jibrilla Bindow ya ba da umarni shimfida hanyoyi masu nisan kilomita 201.4 a kauyen Labando kuma ya ce wannan aikin ya kunshi shimfida hanyoyi biyar a cikin gari.
Ya ce Bankin Duniya da kasar Fransa ne suka ba da kudin aikin, inda ya ce, jihar ta hada kai da wadannan hukumomin ne domin samar wa jama’a saukin safarar kayan gona zuwa kasuwanni. Gwamna ya ce, idan aka kammala hanyoyin za su taimaka wajen inganta samar da hanyoyi a kananan hukumomi wajen samun sauki zuwa asibitoci da sauransu.
Ya ce zai sa ido ya ga an kammala aikin a daidai lokacin da aka kayyade na shekara daya da rabi. Kuma ya ce kwamnatinsa za ta bude wani asusun banki domin sanya irin wannan tallafi a ciki.