Za a kashe Naira biliyan 4.8 wajen yaƙi da cutar HIV a Nijeriya — Ministan Lafiya
Nijeriya ta fi kowacce ƙasa yawan masu cutar a yammacin Afirka.
Majalisar Zartarwa ta ware naira biliyan 4.8 domin yaƙi da yaɗuwar cutar HIV a Nijeriya.
Wannan na daga cikin matsayar da aka cimma a taron Majalisar Zartarwa da ya gudana a ranar Litinin kamar yadda Ministan Lafiya, Farfesa Muhammad Ali Pate ya tabbatar.
- Ma’auratan da aurensu ya mutu sau 12 a shekara 43
- Dalilin da Tinubu ya ƙi amincewa da ƙudirin kafa Jami’ar Ilimi a Adamawa
Ministan ya ce wannan yana daga cikin manufofin gwamnatin na inganta kiwon lafiya a matakin farko.
A cewarsa, an tsara kashe kuɗaɗen ne a fannin ɗaukar ma’aikatan lafiya da ba su horo domin samun ƙwarewa da kuma tabbatar da an bayar da kulawar da ta dace domin hana yaɗuwar cutar HIV a sassan ƙasar.
A yayin da abokan hulɗa daban-daban daga ƙetare sun taka rawar gani wajen yaƙi fa cutar, Farfesa Pate ya ce za ta ƙara zage damtse wajen ɗaukar matakan ceto rayuwar mutanen da ke ɗauke da cutar ta HIV.
A bayan nan dai an riƙa bayyana damuwa game da sabbin tsare-tsaren da gwamnatin shugaban Amurka, Donald Trump ta ɓullo da su, musamman a fannin bayar da tallafi, inda ake tunanin za su iya shafar tallafi ga yaƙi da cutar HIV a ƙasashe masu tasowa.
Amma a ranar Asabar gwamnatin Amurkan ta sanar da ware sabon ƙunshin tallafin yaƙi da cutar ta HIV.
Alƙalumman da hukumar hana yaɗuwar cutar HIV a Nijeriya ta fitar, sun ce ƙasar ce ta fi kowacce yawan masu cutar a yammacin Afirka, kuma an daɗe ana samun kiraye-kiraye daga faɗin duniya na ganin Najeriya ta zage damtse wajen yaƙi da yaɗuwar cutar.