Za a kashe wa Jami’ar Jihar Jigawa Naira biliyan 1.8

Gwamnatin Jihar Jigawa za ta gina gidan shugaban Jami’ar Jihar da dakin taro a harabar jami’ar da ke Kafin Hausa a kan Naira biliyan daya da miliyan 800, don ganin harkokin karatu sun kankama a bana.Kwamashinan Watsa Labarai na Jihar Alhaji Babandi Ibrahim Gumel ya sanar da manema labarai haka jim kadan da kammala taron […]

Za a kashe wa Jami’ar Jihar Jigawa Naira biliyan 1.8
Za a kashe wa Jami’ar Jihar Jigawa Naira biliyan 1.8

Gwamnatin Jihar Jigawa za ta gina gidan shugaban Jami’ar Jihar da dakin taro a harabar jami’ar da ke Kafin Hausa a kan Naira biliyan daya da miliyan 800, don ganin harkokin karatu sun kankama a bana.
Kwamashinan Watsa Labarai na Jihar Alhaji Babandi Ibrahim Gumel ya sanar da manema labarai haka jim kadan da kammala taron Majalisar Zartawar Jihar da Gwamna Sule Lamido ya jagoranta a gidan gwamnati ranar Laraba.
Ya ce tuni aka fara daukar daliban da za su fara karatu a makarantar, inda ya ce gwamnati ta ware Naira miliyan 140 da dubu 300 domin biyan diyyar gonaki da gidajen
mutanen da jami’ar ta shafa.
Ya ce gaba daya gwamnatin jihar za ta kashe Naira biliyan daya da miliyan 800 wajen kan gine-ginen biyu da biyan diyyar gonaki, kuma kauyukan da lamarin zai shafa suna hada da Unguwar Zilawa da Abdallawa da Adaha da Unguwar Dolama da kuma Unguwar Marawa.
Da yake karin haske Kwamashinan Ilimi na Jihar Farfesa Haruna Wakili ya ba da tabbacin cewar jami’ar za ta fara karatu bana, kuma tuni an ba daliban da za su fara karatu guraban karatu a jami’ar.

Daga Umar Akilu Majeri, Dutse