Za a kawo karshen hare-haren Boko Haram nan da watan Afrilu– Babban Hafsan Tsaro

Sabon Babban Hafsan Tsaro (CDS) Iya Mashal Aled Badeh ya ce wajibi ne a kawo karshen hare-haren Boko Haram a Arewa maso Gabas kafin nan da karshen wata Afrilu mai zuwa.Babban Hafsan yana magana ne a wurin bikin karbar aiki daga tsohon Babban Hafsan Tsaro Bayis Admiral Ola Sa’ad Ibrahim a Hedkwatar Tsaro da ke […]

Za a kawo karshen hare-haren Boko Haram nan da watan Afrilu– Babban Hafsan Tsaro

Sabon Babban Hafsan Tsaro (CDS) Iya Mashal Aled Badeh ya ce wajibi ne a kawo karshen hare-haren Boko Haram a Arewa maso Gabas kafin nan da karshen wata Afrilu mai zuwa.
Babban Hafsan yana magana ne a wurin bikin karbar aiki daga tsohon Babban Hafsan Tsaro Bayis Admiral Ola Sa’ad Ibrahim a Hedkwatar Tsaro da ke Abuja, inda ya ce tilas ne a sanya aya ga tabarbarewar tsaro a Arewa maso Gabas kafin Afrilun 2014. “Na shaida wa abokan aikina cewa wajibi ne mu sanya aya ga haka nan da Afrilu ta yadda ba za mu ci gaba da fama da matsalar tsarin mulki ba. Ba mu son mu koma ga Majalisar Dattawa muna roko da kamun kafa. Idan muka yi aiki tare ina ba Janar Minimah tabbacin za ka gama da wannan lamari cikin kankanen lokaci,” inji shi.
Ya kara da cewa”Matasa sun ce akwai mabobin wannan kungiya a cikin sojoji, to ku da kuke nan, ku shaida wa abokanku cewa suna cikin hadari, za mu zo gare ku. Kuma zan yi iyakar kokarina domin jagorantar sojojin Najeriya ga samun nasarar da ake bukata.”
Tsohon Babban Hafsan Admiral Ola Ibrahim ya ce sojojin Najeriya suna tsaye domin karfafa dimokuradiyya ce ba zame mata kafa ba.
Shi kuma Hafsan Hafsoshin Sojan Najeriya Janar Azubuike Ihejirika cewa ya yi manyan hafsoshin soja biyar ne kadai aka shirya za a yi wa ritaya sakamakon nada Janar Minimah ba 30 da wasu jaridu suka ce ba. A wurin mika ragama ga Manjo Janar Minimah, Janar Azuibike Ihejerika ya ce a guji zafafaf harkokin siyasa musamman kan batun hare-hare a Arewa maso Gabas, inda ya ce, babu wani kwamandan soja da zai karfafa wa sojojinsa su rika cin zarafi da keta hakkin jama’ar kasa. A jawabin Janar Kenneth Minimah ya ce sojoji a karkashin jagorancinsa za su ci gaba da kasancewa masu biyayya ga Tsarin Mulkin Najeriya tare da Shugaba Goodluck Jonathan a matsayinsa na Babban Kwamandan Sojojin Najeriya.