Za a kori ’yan Keke-NAPEP daga garin Abuja

Wike ya ce daga watan Disamba sabbin motocin daukar mutane a kwaryar birnin Abuja za su fara aiki

Za a kori ’yan Keke-NAPEP daga garin Abuja

Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya ce daga watan Disamba mai kamawa za a haramta ayyukan baburan Keke-NAPEP a garin Abuja.

Wike ya ce shirye-shirye sun yi nisa domin fito da sabbin motocin daukar mutane a kwaryar birnin Abuja daga wata mai zuwan.

Ya ce da zarar motocin gwamnatin sun fara aiki za a bukaci masu Keke-NAPEP su koma kauyukan Abuja da aiki.

“Na san yanzu matuka Keke-NAPEP za su fara cewa an toshe musu hanyar neman kudi, to amma dole mu dakatar da su domin inganta birnin Abuja, da samar da cikakken tsaro a birnin,” in ji ministan.

Wike ya bayyana hakan ne ranar talata, lokacin da yake ganawa ta musamman da masu tsara taswira da gina gidaje a Abuja, inda ya ce hakan zai rage matsalar tsaro a birnin.

“Ina tabbatar muku idan motocin mu suka fara aiki matsalar kwace a cikin motocin haya za ta kau.

“Motocinmu za su rika zirga-zirga ne a hanyoyin Maitama, Asokoro da sauran sassan kwaryar birnin Abuja” inji Ministan Abuja.

Majalisa ta tsayar da ranar sauraron ra’ayin jama’a kan ƙudirin Dokar Haraji

Abba ya sanya hannu kan dokar kafa rundunar tsaro ta Kano

Za a binciki INEC kan jinkirin gudanar da zaɓen cike giɓi

Gubar harsashi ta jikkata mutane dama a Zamfara