Za a koya wa mata masu ciwon yoyon fitsari sana’o’i a Jihar Katsina

Akalla mata 100 ne wadanda suke fama da ciwon yoyon fitsarin da suka warke za a koyawa sana’a a Jihar Katsina. Kwamishinar harkokin mata ta jihar, Dokta Badiya Hassan Mashi ne ta bayyana hakan a wajen bikin bude koya wa matan sana’o’in a cibiyar da ke asibitin babbar ruga Katsina. A cewarta, wannan shi ne […]

Za a koya wa mata masu ciwon yoyon fitsari sana’o’i a Jihar Katsina

Akalla mata 100 ne wadanda suke fama da ciwon yoyon fitsarin da suka warke za a koyawa sana’a a Jihar Katsina.

Kwamishinar harkokin mata ta jihar, Dokta Badiya Hassan Mashi ne ta bayyana hakan a wajen bikin bude koya wa matan sana’o’in a cibiyar da ke asibitin babbar ruga Katsina. A cewarta, wannan shi ne karo na biyar da za a gudanar da wannan shiri wanda kimanin shekaru hudu da suka wuce ba a samu damar ci gaba da aiwatar da shirin ba sai a wannan lokaci da Gwamna Masari ya sake maido da shirin cikin tsarin gwamnatinsa na koyar da sana’o’i acikin al’umma  ciki har da mata masu wannan lalura ta yoyon fitsari “lallai ne bayan kun kare samun horo a wannan cibiya,  za ku iya dogaro da kanku wajen samun abin yi da kuma inganta zamantakewar ku a halin zaman rayuwa. Don haka muke kara kira a gare ku da ku jajirce ku koyi sana’o’in da ake koya maku don fidda mai girma Gwamna kunya,” inji ta.

Ita dai wannan cibiya an gina ta tun acikin shekarar 2007 wadda kuma ta yaye dalibai mata wadanda suka warke daga wannan lalura ta ciwon yoyon fitsarin har su 355 a cikin kashi hudu na shirin. Har’ila yau, Kwamishinar ta ce gwamnatin Masari ta kashe milyoyin kudi a cikin wannan shekara ta 2017 ta hannun ma’aikatar mata domin koyar da mata 100 da suka fito daga sassa dabam-daban daga ciki da wajen kasar sana’o’i. “Bayan an kammala basu horo, gwamnati ce za ta dauki nauyin basu jarin kayan sana’ar da kowace mace ta koya tare da wasu kudi. Sannan kuma gwamnati ce ta dauki nauyin kai kowace mace har garinsu bayan kammala wannan horo, sannan kuma an tanadar masu komai na rayuwa da suke bukata a lokacin horon.”

Za a koyar da wadannan mata sana’o’in da suka shafi dinki, saka, kiwon kaji, aikin lambu, yin mai da sabulu tare da koyon ilmi na addini da na zamani cikin zama na watanni uku da za su yi a wannan cibiya. Wasu daga cikin matan da zasu amfana da wannan shiri sun bayyana jin dadinsu tare da godiya ga gwamnatin Masari wadda suka ce lallai gwamnatin al’umma ce mai kuma son cigabanta. Malama Amina Batsari ta ce, da farko basu dauka cewar za a cika wannan alkawali ba kamar yadda wasu suke bayyana masu, amma a yau ta tabbatar da cewa duk bayanan da aka rika yi masu a baya ba gaskiya bane a kan wannan gwamnati. Ita ma Halima wadda ta ce ta fito daga karamar Hukumar Chibok da ke Maiduguri ta ce ta ga karamci kuma ta ji dadin yadda aka rika kula da su har Allah Ya sa ta samu sauki ko ta warke daga lalurar yoyon fitsari, sai ga shi kuma ance ba zata koma gida haka nan hannu biyu ba sai an koya mata sana’a kuma ga shi yau abin ya tabbata. Kazalika, Maryamu wadda ta ce ‘yar kasar Nijer ce ita, ta ce tana godiya ga dukkan masu hannu tun daga zaman jiyyar da ta yi har zuwa wannan lokaci da kuma za a koya mata sana’a domin samun abin yi in ta koma gida maimakon zaman banza. Mafi yawan matan da Aminiya ta zanta da su a kan batun zamansu a dakin aure, wasu sun ce za su koma dakin mazajensu domin basu watsar da su ba, yayin da wasu su ka ce za su yi aure in sun samu mazajen da za su aure su sanadiyar rabuwa da mazajensu saboda wannan lalura da suka samu wadda mafi yawa a lokacin da za a haihu ake samunta kamar yadda wata wadda ta nemi a sakaya sunanta ta ce. Matan dai sun yi kira ga maza da su rika rungumar kaddara a duk lokacin da suka ga matansu sun samu wannan lalura wadda take faruwa daga dakunansu na aure.