Za a kwaso ’yan Najeriya kusan 300 daga Afirka ta Kudu ranar Laraba

Wasu ’yan ƙasar Afirka ta Kudu na zargin baƙin haure da ƙwace musu guraben aiki da kuma aikata miyagun laifuka.

Za a kwaso ’yan Najeriya kusan 300 daga Afirka ta Kudu ranar Laraba

Babban Ofishin Jakadancin Najeriya da ke Pretoria tare da Ofishin Jakadancin Ƙasar da ke Johannesburg sun sanar da shirin dawo da ’yan Najeriya 271 daga Afirka ta Kudu a ranar Laraba.

Hakan na cikin wata sanarwa mai ƙunshe da jerin sunayen waɗanda za a kwaso, wadda Babban Jami’in Jakadancin Najeriya a Johannesburg, Ninikanwa Okey-Uche, ya fitar a ranar Litinin.

Sanarwar ta ce jirgi na musamman wanda shi ne zai kasance sahu na huɗu da gwamnatin Najeriya ta tanada domin dawo da ’yan ƙasar zai tashi daga Filin Jirgin Sama na O.R. Tambo da ke Johannesburg da sanyin safiyar ranar Laraba.

Ta ƙara da cewa jami’an jakadancin za su kira duk waɗanda aka zaɓa domin sanar da su cikakkun bayanan tafiyar.

Babban Jami’in Jakadancin ya umarci duk masu shirin dawowa gida da su hallara a Ofishin Jakadancin Najeriya da ke Pretoria da ƙarfe 10:00 na safiyar ranar Talata domin shirye-shiryen tafiyar.

Ofishin ya kuma buƙaci su taru domin a ɗauke su cikin motocin bas da ofisoshin jakadancin suka tanada, domin tabbatar da tsaron lafiyarsu da kuma ba su damar shiga wani keɓaɓɓen wuri da aka ware domin kammala duk wasu ƙa’idojin ficewa daga ƙasar.

Sanarwar ta yi gargaɗin cewa duk wanda ya zaɓi zuwa filin jirgin da kansa ba za a ba shi damar shiga wannan keɓaɓɓen wuri ba, kuma hakan na iya hana shi kammala dukkan matakan da ake buƙata na dawo da shi gida.

A bayan nan ne Gwamnatin Najeriya ta ɗauki matakin kwaso ’yan kasarta zuwa gida a sakamakon barazanar da rayuwarsu ke fuskanta a dalilin tsangwamar baƙi a Afirka ta Kudu.

Tun daga watan Afrilun da ya gabata dai aka soma shafe makonni ana gudanar da zanga-zangar ƙin jinin baƙi a sassan Afirka ta Kudu, lamarin da ya ƙara haifar da taƙaddama tsakanin ’yan kasar da ma’aikata ’yan ƙasashen ƙetare.

Wasu ’yan ƙasar ta Afirka ta Kudu na zargin baƙin haure da ƙwace musu guraben aiki, yayin da hukumomin ƙasar suka yi Allah wadai da zanga-zangar, suna mai bayyana ta a matsayin nuna ƙyamar baƙi.