Za a magance zaman yara a titi kafin karshen 2017
Babban Sakataren Hukumar Ilimin Baidaya, (UBEC), Alhaji Dikko Sulaiman, ya ce, hukumarsa ta dauki matakai don sanya yaran da ke gararamba a kan titi makarantar boko kafin karshen 2017. Ya yi furucin ne yayin da yake tattaunawa da manema labarai, jim kadan bayan ya karbi rahoto daga kwamitin da ya kafa don tsara dabarun da […]
Babban Sakataren Hukumar Ilimin Baidaya, (UBEC), Alhaji Dikko Sulaiman, ya ce, hukumarsa ta dauki matakai don sanya yaran da ke gararamba a kan titi makarantar boko kafin karshen 2017.
Ya yi furucin ne yayin da yake tattaunawa da manema labarai, jim kadan bayan ya karbi rahoto daga kwamitin da ya kafa don tsara dabarun da ma’aikatarsa za ta bi wajen tunkarar kalubalen ilimi a cikin shekaru biyar, wanda aka gudanar a hedikwatar hukumar UBEC da ke Abuja a cikin makon da muke ciki.
Ya ce, hukumar a matsayinta na mai shiga tsakani, ta bullo da shirye-shirye masu yawa don ganin ta cin ma burinta na ganin miliyoyin yaran da ke yawo a kan titi sun koma makaranta kafin karshen shekara 2017.
“Ina mai tabbatar muku da cewa kafin karshen shekarar 2017, ba za sake samun yara suna gararamba a kan titi ba saboda dukkaninsu za mu tabbatar an sanya su a makaranta.” Inji shi.
Ya bayyana cewa shirye-shiryen da suka bullo da su sun hada da gina makarantu da tsara manhajar ilimi da za su jawo hankulan yara, don su rika zuwa makaranta, su zauna su koyi ilimi.
Ya ci gaba da cewa sun bullo da shirin ilimin zamani, wanda ya dace da tsarin almajirai da tunaninsu da kuma fahimta.
Sannan kuma ya kara da cewa sun bullo da shiri inda suka gina makarantu tare da tsara manhajar ilimin koyon sana’o’i da yaran da ba su zuwa makaranta a yankin Kudu maso gabas da kuma yankin Kudu maso kudu.
Ya ce wadannan shirye-shirye za su taimaka kwarai da gaske wajen cin ma burin da hukumar ta sanya a gaba na sanya dukkanin yaran da ke gararamba akan titunan kasar nan makaranta nan da shekarar 2017.
Da yake jawabi, shugaban kwamitin tsara dabarun da hukumar ilimin baidaya za ta bi wajen tunkarar kalubalen ilimi, Farfesa Umar Tuni Muhammad, ya ce shawarar da suka bayar ta hada da mayar da hankali wajen shiga tsakani da hukumar take yi na inganta ilimi da tattaunwa da masu ruwa da tsaki da kuma maganin matsalolin da ke addabar ilimi tare da bayar da muhimmanci ga burin da aka so a cin mawa.