Za a mayar da gidan yarin da ya haura shekara 100 zuwa gidan tarihi a Kano

Za a mayar da dukkan fursunonin da ke tsare zuwa sabon gidan gyaran hali na zamani daura da barikin sojoji da ke Janguza.

Za a mayar da gidan yarin da ya haura shekara 100 zuwa gidan tarihi a Kano

Kofar shiga Gidan Yarin Kurmawa

Gwamnatin Kano ta bayyana shirin mayar da tsohon gidan yarin nan na Kurmawa, wanda aka gina fiye da shekara 100 da suka gabata, zuwa gidan adana abubuwan tarihi.

Gidan yarin Kurmawa mai ɗaukar fursunoni 690 kacal, wanda aka gina a shekarar 1910 tun a zamanin Turawan mulkin mallaka a kusa da fadar mai martaba Sarkin Kano, yana da tarihin shekaru 115.

Mai ba Gwamnan Kano shawara kan harkokin yaɗa labarai, Ibrahim Adam, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi.

Hadimin gwamnan ya ce an yanke shawarar sauya ma’anar wurin, daga gidan yari zuwa wuri na musamman da za a taskance abubuwan tarihi da suka shafi mulkin mallaka da kuma tarihin Jihar Kano.

A cewarsa, za a mayar da dukkan fursunonin da ke tsare a Kurmawa zuwa sabon gidan gyaran hali na zamani, wanda ke kan babbar hanyar Kano zuwa Gwarzo, a kusa da barikin sojoji da ke Janguza.

Wannan sabon gidan yari wanda aka gina shi ne a zamanin gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, yana da ƙarfin ɗaukar fursunoni kusan 3,000.

Shirin na mayar da Kurmawa gidan tarihi, na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin Kano na raya wuraren tarihi da al’adu, da kuma cusa wa al’umma sha’awar sanin tarihi da adana shi yadda ya kamata.