Za a maye gurbin shugaban karamar hukumar Garko

Sakamakon bacewar Shugaban karamar Hukumar Garko, Jihar Kano, Mazayyani Hamza Sa’id, za a kaddamar da mataimakinsa a matsayin mukaddashi, sakamakon samun amincewar majalisar dokokin jihar, cewa ya ci gaba da jagorancin karamar hukumar kafin a sami sahihin bayani kan zababben shugaban. Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana haka ranar Larabar da ta […]

Za a maye gurbin shugaban karamar hukumar Garko
Za a maye gurbin shugaban karamar hukumar Garko

Sakamakon bacewar Shugaban karamar Hukumar Garko, Jihar Kano, Mazayyani Hamza Sa’id, za a kaddamar da mataimakinsa a matsayin mukaddashi, sakamakon samun amincewar majalisar dokokin jihar, cewa ya ci gaba da jagorancin karamar hukumar kafin a sami sahihin bayani kan zababben shugaban.

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana haka ranar Larabar da ta gabata, a fadar gwamnati, yayin da ya rantsar da Mataimakin Shugaban karamar Hukumar Kabo, Alhaji Mamuda Idris Kabo a matsayin sabon shugaban karamar hukumar; sakamakon nadin da aka yi wa zababben shugaban karamar hukumar a matsayin Kwamishinan kananan hukumomin jihar ta Kano.
Gwamnan ya kara da cewa Shugaban karamar Hukumar ta Garko, Hamza Sa’id ya bace ne a kasa mai tsarki, tun lokacin da aka sami turmutsitsi a wajen jifar Shaidan a Saudiyya kuma har ya zuwa wannan lokaci babu wani sahihin bayani a kansa, wanda hakan ta sanya za a rantsar da mataimakinsa a matsayin mukaddashi.