Za a mika mulki ga farar hula a Burkina Faso cikin mako biyu – Afirka ta Yamma
Sojojin da suka karbe mulki bayan masu zanga-zanga sun tursasa Shugaba Blaise Compaore ya ajiye mulkin kasar Burkina Faso, sun yi ikrarin mika mulki ga farar hula cikin mako biyu. Al’amarin kuwa ya biyo bayan tursasawar da suka samu daga kasashen duniya, musamman Amurka da kasashen kungiyar Tattalin Arzikin Arzikin Afirka ta Yamma. kasar Faransa […]
Sojojin da suka karbe mulki bayan masu zanga-zanga sun tursasa Shugaba Blaise Compaore ya ajiye mulkin kasar Burkina Faso, sun yi ikrarin mika mulki ga farar hula cikin mako biyu. Al’amarin kuwa ya biyo bayan tursasawar da suka samu daga kasashen duniya, musamman Amurka da kasashen kungiyar Tattalin Arzikin Arzikin Afirka ta Yamma.
kasar Faransa ta taimaka wa Compaore ya arrce zuwa kasar Ibory Coast, bayan day a shafe shekara 27 yana mulkin kasar,amma da ya yi yunkurin amfani da majalisar kasar don ta kara masa wa’adi ya yi tazarce, sai zanga-zangar adawa ta yi awon gaba da mulkinsa.
Shugabannin kasashen kungiyar bunkasa Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma (ECOWAS), karkashin jagorancin Shugaban kasar Ghana, John Dramani Mahama ta isa kasar, tare da shugabannin Najeriya da Senegal, don tattaunawa da jam’iyyun adawa da Shugaban mulkin soja, Laftanar Kanar Isaac Zida.
Bayan an cimma yarjejeniyar mika mulki bayan mako biyu,kamar yadda Zida ya bayyana, cewa: “Idan kowa ya amince ban ga dalilin da zai sanya ba za amika mulkin ba,cikin mako biyu,” kamar yadda kakakin kungiyar Afirka ta Yamma Joseph Tiendrebeogo ya tabbatar.
Shi ma shugaban babbar kabilar Mossi, Mogho Naba ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP cewa Zida ya yi alkawarin mika mulki ga shugabannin al’umma, a gaban jakadun kasashen duniya.