Za a mika mulki ga sabuwar gwamnatin Myanmar
Shugabar ‘yan adawar kasar Myanmar (wanda wasu suke kira Bama) Aung San Suu Kyi da Shugaban kasar Mai barin gado Thein Sein, sun amince da tsarin mika mulki ga sabuwar gwamnatin kasar cikin kwanciyar hankali.A shekaranjiya Laraba ne dai shugabannin biyu suka amince da wannan tsarin na mika mulkin ba tare da tashin hankali ba […]
Shugabar ‘yan adawar kasar Myanmar (wanda wasu suke kira Bama) Aung San Suu Kyi da Shugaban kasar Mai barin gado Thein Sein, sun amince da tsarin mika mulki ga sabuwar gwamnatin kasar cikin kwanciyar hankali.
A shekaranjiya Laraba ne dai shugabannin biyu suka amince da wannan tsarin na mika mulkin ba tare da tashin hankali ba bayan sun shafe kimanin minti 45 suna tattaunawa da juna a fadar shugaban kasar, kamar yadda kafar yada labarai ta RFI ta bayyana.
Wannan dai na zuwa makonni uku da bayyana jam’iyyar NLD ta Suu Kyi a matsayin wadda ta lashe zaben kasar, kuma a karon farko ke nan da bangarorin biyu suka gudanar da irin wannan tattaunawar tun bayan lashe zaben.
Jam’iyyar dai ta lashe kusan kashi 80 cikin 100 na zaben wanda aka gudanar a ranar 8 ga watan Nuwamba da ya wuce, abin da ake ganin zai kawo karshen mulkin sojin kasar na tsawon shekaru.
Dama dai jim kadan da lashe zaben ne, Suu Kyi ta bukaci ganawa da Shugaba Sein kan yadda za su fahimci juna kuma shugaban ya yi alkawarin mika ragamar mulki ga duk wanda ya yi nasara.
A bangare guda, Suu Kyi ta gana da kwamandan sojin kasar Janar Min Aung Hlaing, inda suka shafe kusan sa’a guda suna tattauanawa.
A shekarar 1990 dai jam’iyyar NLD ta taba samun nasara a zaben kasar, amma sojoji suka yi fatali da sakamkon zaben, tare da ci gaba da rike madafun ikon kasar.