Za a nada ministan sanya farin ciki a Hadaddiyar Daular Larabawa
A nan gaba kasar Hadaddiyar Daular Larabawa za ta nada ministan cusa wa ’yan kasa farin ciki, cewar Firayiministan kasar.Firayiministan Hadaddiyar Daular Larabawa uya ce za ta fitar da hannunta wajen gudanar da wasu ayyukan gwamnati, sannan ta nada ministan da za a dora wa alhakin cusa wa al’ummar kasr farin ciki.Sheikh Mohammed bin Rashid […]
A nan gaba kasar Hadaddiyar Daular Larabawa za ta nada ministan cusa wa ’yan kasa farin ciki, cewar Firayiministan kasar.
Firayiministan Hadaddiyar Daular Larabawa uya ce za ta fitar da hannunta wajen gudanar da wasu ayyukan gwamnati, sannan ta nada ministan da za a dora wa alhakin cusa wa al’ummar kasr farin ciki.
Sheikh Mohammed bin Rashid Al Maktoum, wanda shi ne Sarkin Dubai, ya yi wadannan kalamai ne, a taron gwamnatocin duniya da kasarsa ta dauki nauyi.
Ya ce za a hade wasu ma’aikatun gwamnati, sannan za a nada ministan da zai kula da hakuri da juna a wanann kasa da ke yankin Tekun Fasha, wadda ta zama wurin gwamuwar addinai da al’adu iri-iri.
A wani sakon da ya aike ta shafinsa na twitter, cewa ya yi, za a kulla alaka a tsakanin tsare-tsaren gwamnati, don samar da walwala da kyautata jin dadin al’umma.
“Wannan sabuwar tafiya ce ta cimma buri don kyautata wa mutare, saboda haka muna rokon Allah ya taimake mu, mu yi hidima, wajen kula da su,” kamar yadda yake kunshe a sakon sa.
daukacin skonnin da ya aike ba su yi nuni kan loklacin da za a aiwatar da sababbin tsare-tsaren da ya bijiro da su ba.
Sai dai wannan yunkurin na sheikh Muhammad, a daidai lokacin da shekarun sa suka cika 66 sun tattare ne wajen sanya wa al’ummar kasar farin ciki, al’amarin da ake sa rana aiwatarwa nan gaba a tsawon lokaci da nufi na gaskiya keke da keke.
Sheikh Muhammad ya ce yunkurinsa na kawo sauyi a tsarin gwamnatin tarayya, ya bijiro da shi ne bayan da ya tuntubi Sheikh Mohammad Zayed Al Nahayan, yarima mai jiran gado a masarautar Abu Dhabi. Shafin sadarwar gidan talabijin na Aljazeera day a ruwaito labarin bai fayyace lokacin da za a nada ministan ba, ko kuma yadda zai rika cusa farin ciki a zukatan dimbin al’ummar kasar.
Ita kuwa jaridar Arabnews ta ruwaito yadda Firayiministan ya kudurin aniyar nada ministan matasa, wanda shekarunsa ba su wuce 22, kuma ma’aikatar kula da harkokin matasan za ta kasance karkashin kulawar minista mace.
“Wadannan matasa maza da mata, za su rika bai wa gwamnati shawara kan al’amuran da suka shafi matasa, inda majalisar matasan za ta kasance karkashin shugabancin macen da shekarunta ba su wuce 22,” inji shi. Domin a cewarsa: “Matasa su ne karfin gwamnatin mu nan gaba.”