Za a raba wa manoma injin ban ruwa mai aiki da hasken rana a Kebbi
Manoman rani 10,000 za su samu injinan ban ruwa masu aiki da haske rana
Gwamnatin Kebbi za ta raba wa manoman rani 10,000 injinan ban ruwa masu aiki da haske rana domin saukake masu harkokin noma a jihar.
Gwamnan jihar, Dakta Nasir Idris ya sanar da cewa Ministan Noma ne zai zo jihar a ranar Alhamis domin kaddamar da rabon tallafin da gwamnati ta samar.
A cewarsa, ministan zai kaddamar da injinan ban ruwa na ‘sola’ guda 10,000 ga manoma a fadin Jihar Kebbi.
Ya bayyana cewa an samar da injin na ‘sola’ ne ganin yadda man fetur ya yi tsada, kuma yana son jihar Kebbi ta ci gaba da rike kambinta a matsayin jagaba wurin samar da shinkafa a Nijeriya.
Gwamnan ya ce gwamnatinsa za ta cigaba da ba da tallafin abubuwan da za su sanya harkar noma ta yi sauki ga manoma.
Mai shi shawara kan harkokin yada labarai, Yahaya Sarki ne ya fitar da bayanin cikin sanarwar zuwan ministan a wannan satin.