Za a raba wa manoma tallafin Naira biliyan 600

Manoma miliyan 2.4 za su amfana da rance mara ruwa, inji Buhari.

Za a raba wa manoma tallafin Naira biliyan 600

Manoma

Gwamnatin Tarayya za ta raba wa namoma bashi mara ruwa na Naira biliyan 600 a yunkurinta na wadata kasa da abinci.

Shugaba Muhammadu Buhari ne ya sanar cewa manoma miliyan 2.4 ne za su amfana da rancen tallafin a fadin Najeriya karkashin shirin bunkasa samar da amfanin gona (APPEALS).

Ya ba da sanarwar ce a taron bikin baje kolin kayan goma da aka shirya domin bikin Ranar Abinci ta Duniya ta shekarar 2021 a Abuja.

Buhari ya yi bayanin ne ta bakin Ministan Noma da Raya Karkara, Mohammed Abubakar, wanda ya wakilce shi a taron wanda ya gudana a ranar Laraba.

Taken taron na bana shi ne “Ayyukanmu su ne rayuwarmu ta gaba: Samar da wadataccen abinci, Karin lafiyayyen abinci, muhalli da kuma rayuwa mai inganci”.

A nasa jawabin, Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Harkokin Noma, Sanata Abdullahi Adamu, ya ce gwamnatin Buhari ta jima tana bullo da manufofi da tsare-tsare domin samar da wadaccen abinci a Najeriya.