Za mu rabe Kwalejojin Tarayya 115 da ke Najeriya —Minista
Nan ba da jimawa ba za ta raba makarantun sakandaren tarayya guda 115 da ke faɗin Najeriya
Gwamnatin Tarayya ta sanar cewa nan ba da jimawa ba za ta raba makarantun sakandaren tarayya guda 115 da ke faɗin ƙasar nan.
Ƙaramin Ministan Ilimi, Dakta Yusuf Sununu, ya bayyana cewa za a raba kwalejojin ne zuwa ƙanana da manyan makarantun gaba da sakandare.
Dakta Yusuf Sununu ya bayyana haka ne yayin buɗe Taron Shekara-shekara na Shugabannin Kwalejojin Tarayya a Abuja ranar Talata.
Taken taron shi ne: “Iliman Harkokin Kasuwanci: Hanyar Dogaro da Kai da Ci gaban Ƙasa.”
- Kamaru ta buɗe Madatsar Lagdo: Jihohin 11 Najeriya su shirya wa ambaliya —Gwamnati
- Sojoji sun kashe ’yan bindiga 4 sun ceto mutane 20 a Kaduna
Sununu ya bayyana cewa shirin raba kwalejojin ya yi daidai da Tsarin Ilimi na Ƙasa.
Ya bayyana cewa, rarrabe kwalejojin zai haɗa da samar da ƙarin kuɗaɗe don inganta kayan aiki, inganta jin daɗin malamai, da samar da ayyukan yi.
Ya ƙara da cewa ma’aikatar tare da goyon bayan hukumomin gwamnati da abin ya shafa, za ta tabbatar da an cimma hakan cikin ƙanƙanin lokaci.
Sununu ya yi kira da a haɗa kai da shugabannin makarantun a matsayinau na masu ruwa da tsaki don inganta yanayin ilimi a makarantun.
Shugaban Shugabannin Kwalejojin Tarayya, Dokta Idowu Akinbamijo, ya ce taron na da nufin tsara ajandar da za a yi a shekara mai zuwa da kuma kara karfin ayyukan da ke gabansu.