Za a rage albashin manyan ma’aikata a Tanzaniya

Shugaban kasar Tanzaniya John Magufuli ya sha alwashin zabtare albashin manyan ma’aikatan gwamnati a kasar.Ya shaida wa magoya bayansa cewa ba za a yadda a ce ana biyan wasu jami’ai Dala dubu 18 a wata yayin da ake biyan kananan ma’aikata Dala 140 ba kacal.Mista Magafuli ya ce zai kayyade albashin manyan ma’aikatan zuwa kimanin […]

Za a rage albashin manyan ma’aikata a Tanzaniya
Za a rage albashin manyan ma’aikata a Tanzaniya

Shugaban kasar Tanzaniya John Magufuli ya sha alwashin zabtare albashin manyan ma’aikatan gwamnati a kasar.
Ya shaida wa magoya bayansa cewa ba za a yadda a ce ana biyan wasu jami’ai Dala dubu 18 a wata yayin da ake biyan kananan ma’aikata Dala 140 ba kacal.
Mista Magafuli ya ce zai kayyade albashin manyan ma’aikatan zuwa kimanin Dala dubu bakwai a wata.
Shugaban ya yi alkawarin cewa zai rage barnar da ake yi a gwamnati, a lokacin mulkinsa.
A farkon watan nan ne Ma’aikatar Sufuri da Sadarwa ta kasar ta gargadi ma’aikatanta cewa za su iya rasa aikinsu, idan suna amfani da shafukan zumunta na zamani.
Minista a Ma’aikatar Makame Mbarawa, ya ce gargadin zai taimaka wajen ingantuwar aiki da kuma kaucewa raba hankali a tsakanin ma’aikatan a lokacin aiki.
Kamfanin wayoyin salula na samar da Intanet ga jama’a a Tanzaniya a kan farashi mai rahusa, abin da ya sa shafuka kamarsu WhatsApp da Facebook da Twitter da Instagram suke da farin jini a tsakanin al’ummar kasar.