Za a rataye dan fashin da ya saci kwalaban giya bakwai
Babbar Kotun Ado Ekiti ta yanke hukumcin kisa ta hanyar rataya ga Raji Babatunde da aka same shi da aikata laifin yin amfani da adda da wuka da ya tsoratar da Mudashiru Bello da Oladele Femi, sannan ya kwace kwalaban giya guda bakwai da wayoyin salula guda uku daga hannunsu. Da yake zartas da hukumcin […]
Babbar Kotun Ado Ekiti ta yanke hukumcin kisa ta hanyar rataya ga Raji Babatunde da aka same shi da aikata laifin yin amfani da adda da wuka da ya tsoratar da Mudashiru Bello da Oladele Femi, sannan ya kwace kwalaban giya guda bakwai da wayoyin salula guda uku daga hannunsu.
Da yake zartas da hukumcin a ranar Larabar makon jiya a garin Ado Ekiti, Alkalin kotun, Mai Shari’a Cornelius Akintayo ya ce duk da yake wanda ake zargin bai amsa laifinsa ba, amma kotu ta gamsu da shaidun da aka gabatar gabanta da suka tabbatar da aikata wannan laifi na fashi da makami da aka tuhumi Raji Babatunde da aikatawa.
Saboda rashin tabbatattun shaidu, Alkalin ya sallami mutum na biyu mai suna Sunday Adegboye da ake tuhumarsu tare da mai laifin da aka samu da aikata fashi da makami a unguwannin Odundun da Okesa da Dallimore duka a garin Ado Ekiti.
A can Jihar Osun kuwa, Alkalin Kotun Majastare ta Osogbo ne Mai Shari’a O. A. Oloyede ya yanke hukumcin daurin shekara daya ga wata matar aure mai shekaru 35 mai suna Nafisat Raji saboda laifin satar wayar salula mai darajar kudi Naira dubu 15.
An gurfanar da Nafisat Raji mai ‘ya’ya uku gaban kotu ne ba tare da lauyan kariya ba, a inda ta amsa aikata laifin da aka tuhume ta tare da neman saukin hukumci saboda karancin shekaru na karamar diyarta da take goyo. A dalilin haka Alkalin ya yanke mata hukumcin biyan tarar kudi naira dubu 10 ko daurin shekara daya a gidan yari idan ta gaza biyan tarar.
Aminiya ta jiyo ra’ayoyin wasu mutane dangane da wadannan hukumci biyu da kotunan Najeriya suka yanke wa mutanen da suka tabbatar da aikata laifin fashi da makami da sata. Wasu daga cikin ra’ayoyin sun yi na’am da hukumcin kamar yadda dokokin kasa suka shimfida a yayin da wasu suke ganin ya kamata majalisun dokokin tarayya suyi gyara a kan irin wadannan dokoki. Masu wannan ra’ayi cewa suka yi akwai gyara akan yadda kotuna suke yanke hukumci mai tsanani ga masu aikata kananan laifuka da yin sako sako ga masu manyan laifuka.
Matawallen Ibadan, Alhaji Aminu Harande cewa ya yi “Hakika dokar kasa ta yi tanadin hukumci iri daya ne ga dukkan wanda ya yi amfani da makami wajen tsoratar da mutane da kwace dukiyarsu ba tare da lura da yawan dukiyar ko karancinta ba. Amma wasu mutane suna ganin kamata ya yi a bambamta irin hukumcin da za a yanke ga mai satar kananan abubuwa da manya. Ina ganin akwai yiwuwar yin gyara ga abun da mafi yawancin jama’a suke so ayi.”
Shi kuwa Ustaz Tahir Zubairu cewa ya yi “rashin yin adalci ga masu aikata karami da babban laifi shi ne yake haifar da matsala da jama’a suke kallon ba ayi daidai ba. Adalci shi ne yanke hukumci daidai da irin laifin da mutum ya aikata karami ko babba.”