Za a rataye dan sandan da ya kashe lauya mai juna biyu

Kotu ta yanke wa wani dan sanda hukuncin kisa ta hanyar ratayewa kan laifin harbe wata lauya mai juna biyu

Za a rataye dan sandan da ya kashe lauya mai juna biyu

Kotu ta yanke wa wani dan sanda hukuncin kisa ta hanyar ratayewa kan laifin harbe wata lauya mai juna biyu har lahira.

Mai Shari’a Ibironke Harrison ta Babbar Kotun Jihar Legas ta yanke wa ASP Drambi Vandi, hukuncin ne bayan da ta same da da laifin kisan wata lauya mai juna biyu, Omobolanle Raheem a ranaar Kirsimeti.

Gwamantin jihar ce ta gurfanar da ASP Vandi kan harbi mai juna biyun da ya yi a ranar 25 ga Disamba, 2022 a yankin Ajah karkashin gada.

Kisan gillan ya tayar da kura musamman a kafofin sada zumunta, har ta kai ga an hukumar ’yan sanda dakatar da dan jami’in daga aiki, aka gurfanar da shi a kotu.

A yayin zaman kotun, masu gagabar da kara sun gabatar da shaidu 11, ciki har da ’yan sanda takwas da hujjoji 27 a kan wanda ake zargin.

Mai shari’a Ibironke Harrison ta ce shaidun sun ba da gamsassun hujjojin da ke tabbatar da cewa dan sandan ne ya kashe lauyar.