Za a rataye matar da aka samu da laifin taimaka wa ’yan bindiga a Katsina
A shekarar 2023 aka kama matar a tashar mota ta Jibia tana ƙoƙarin kai wa wani jagoran ’yan bindiga alburusai.
Babbar Kotun Tarayya da ke Katsina ta yanke wa wata mata, Hauwa’u Mukhtar hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samun ta da laifin haɗa baki da kuma taimaka wa ayyukan ta’addanci.
An kama Hauwa’u ne a tashar mota ta Jibia a ranar 16 ga Satumbar 2023, yayin da ake zargin tana ƙoƙarin kai wa wani jagoran ’yan bindiga alburusai.
- Real Madrid ta tsawaita kwantaragin Rudiger zuwa baɗi
- ’Yan bindiga sun kashe manoma 4, sun sace 12 a Sakkwato
Mai Shari’a A.B. Bawale ya ce masu gabatar da ƙara sun tabbatar da tuhume-tuhumen da ake yi wa mata ta hanyar shaidu da hujjojin da aka gabatar a kotu.
Bisa haka ne kotun ta same ta da laifi a dukkan tuhume-tuhumen, sannan ta yanke mata hukuncin kisa kamar yadda dokar hukunta laifuffuka ta Jihar Katsina ta tanada.
Hukuncin na zuwa ne makonni biyu bayan wata kotu a Abuja ta yanke wa wasu mutum huɗu hukuncin kisa saboda hannu a harin ta’addancin da aka kai Cocin St. Francis da ke Owo a Jihar Ondo a shekarar 2022.