Za a rataye matasa biyu kan laifin fashi da makami a Uyo

Matasan biyu sun shahara wajen yin amfani da keke napep wajen yi wa mutane fashi da makami.

Za a rataye matasa biyu kan laifin fashi da makami a Uyo

Wasu ‘yan fashi biyu da suka shahara wajen yin amfani da babu mai kafa uku wanda aka fi sani da Keke Napep wajen yi wa mutane fashi suna kwatar dukiyarsu, za su bakunci lahira ta hanyar rataya.

An ce barayin su uku ne a gungunsu, inda sukan bibiyi shige-da-ficen jama’a a bankuna da wuraren na’urorin cire kudi na ATM suna yi musu fashi.

Babbar Kotun Jihar Akwa Ibom mai zamanta a Uyo ce ta yanke wannan hukunci, bayan da biyu daga cikin ‘yan fashin da suka shiga hannu suka amsa laifin da ake tuhumarsu.

Ababen zargin su fada wa kotun cewa sun saba haduwa ne a Sakatariyar Tarayya da ke Uyo, sannan su tsara yadda harkokinsu na wannan rana za su gudana kafin su bazama bibiyar bankuna da wuraren ATM suna la’akari da mutanen da suka ciro kudi.

Kotun ta samu Donald John Obot dan asalin yankin Nung Obong da ke Karamar Hukumar Nsit Ubium da kuma Blessing Christopher Utah, daga Ibiaku Uruan a Karamar Hukumar Uruan ta jihar Uyon, da aikata lafin yi wa wata ‘yar kasuwa mai suna Esther Victor Akpan fashi.

Bayanai sun nuna matasan sun yi wa Akpan fashi ne tun a Disamban 2018 bayan ta ciro kudi Naira dubu 110 daga bankin da take ajiyar kudadenta.

Kazalika, an ce sun kuma kwace N500,000 da N200,000 daga hannun wasu mutum biyu, sai kuma wata mata da ita ma aka ce sun karbe mata N130,000 a kan hanyar IBB da ke Uyo.

Da yake zartar da hukunci, Alkalin kotun, Mai Shari’a Okon Okon ya samu Donald Obot da Blessing Utah da laifin hadin baki wajen cutarwa da kuma laifin fashi da makami.

Alkalin ya ce abin takaici ne yadda ‘yan fashi da makami suka mayar da hanyar zirga-zirgar jama’a ta fashi da makami inda suka yi amfani da babu mai kafa uku wajen aikata miyagun laifuka.

A karshe Alkalin ya yanke wa su biyun da suke kare kansu hukuncin kisa ta hanyar rataya, yana mai yi musu addu’ar Allah Ya jikansu.

Dangane da shugaban gungun ‘yan fashin wanda ya tsere ba a samu an kama shi ba, Alkalin ya ce kwanakinsa kidayayyu ne, kuma zai fi kyau ya yi amfani da wannan dama wajen gyara abin da ya rage na rayuwarsa.