Za a rataye mutane 3 kan kisan kwamandan soji

Kotu ta ƙara musu da ɗaurin shekaru 14 bayan samun su da laifin kisan Kanar Anthony Okeyin bayan sun yi masa fashi da makami a cikin barikin sojoji

Za a rataye mutane 3 kan kisan kwamandan soji

(Hoto: us.fotolia.com)

Kotu ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wasu mutane uku da ta samu da laifin kashe Kanar Anthony Okeyin, Kwamandan Makarantar Sakandare ta Sojoji da ke Apata a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo.

A zaman Babbar Kotun Jihar Oyo  a ranar Talata a Ibadan, Mai Shari’a Ezekiel Ajayi, ya ƙara musu da ɗaurin shekaru 14 saboda aikata laifin haɗa baki da fashi da makami.

Mutum ukun — Agada Solomon da Taiwo Adeniyi da Bibisoye Kehinde — suna daga cikin mutane shida da aka gurfanar a kan kisan babban hafsan sojan a ranar 12 ga watan Disamba na shekarar 2016.

Alkali Ajayi ya yanke hukuncin ne bayan samun tabbatattun shaidu da iƙirarin aikata laifin da waɗanda ake zargin suka yi da bakinsu da kuma gano wayar hannu mallakar Marigayi Kanar Anthony Okeyin a hannun ɗaya daga cikinsu mai suna Agada Solomon.

Sai dai kotun ta sallami ragowar mutane ukun — suna Ewere Andrew da Udobata Oruza-Uzie da Ephraim Obi — saboda ba ta same su da laifi a kan kisan gillar da aka yi wa babban hafsan sojan ba.

Amma ta ce ɗaya daga cikinsu, Ephraim Obi ne kaɗai aka danganta shi da laifin a dalilin yin amfani da motarsa da aka yi wajen aikata laifin.

A lokacin zaman kotun, lauyar masu gabatar da ƙara, Misis K.K. Oloso, ta shaidawa alƙalin cewa waɗanda ake zargin sun yi wa Kanar Anthony Okeyin kisan gillar ne a rukunin gidajen Sojoji (Commandant’s Quarters), inda suka ƙwace wayarsa ƙirar Samsung X4 da ke hannunsa, ta hanyar fashi da makami.

Tunda farko sai da lauya mai kare waɗanda ake zargi, F.O. Awonusi, ya roƙi kotun ta yi adalci kuma ta sassauta hukumcinta a kan waɗanda yake karewa.

Amma Alƙali Ajayi ya yi watsi da wannan buƙatar.

Duk da man Dangote, wahalar fetur ta dawo a Abuja

Za a rataye mutane 3 kan kisan kwamandan soji

DAGA LARABA: Dalilin Da ’Yan Najeriya Ke Buga-Buga Ko Da Suna Aikin Albashi?

UNICEF ta tallafa wa Kano da kayan adana alluran rigakafi