Za a rataye shi saboda kisan jariri

Kotu ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wani wanda ya kashe jariri dan wata shida da haihuwa.

Za a rataye shi saboda kisan jariri

Zama Kotu. (Hoto: Aminiya)

Kotu ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wani wanda ya kashe jariri dan wata shida da haihuwa saboda wayar salula.

Mai Shari’a Marcel Okoh ta Babbar Kotun Jihar Delta ta ya ke wa Obinna Eze hukuncin ne bayan samun sa da laifin kisan jaririn ta hanyar saran sa da adda da kuma ji masa munanan raunuka.

A watan Oktoban shekarar 2023 ne Eze da mahaifiyar jaririn, Misis Blessing Igwe, suka samu saɓani kan ɓacewar waya a gidan da suke zaune.

A sakamakon haka ne Obinna Eze ya ɗauko adda ya sassare ta da jaririn nata, lamarin da ya yi ajalin jaririn bayan mako guda a asibitin da aka yi jinyar su.

Likitan da ya duba su, Dakta  Emmanuel Egbuduka, ya alaƙanta rasuwar jaririn da munanan sara uku da aka yi wa jaririn a ka.

Bayan sauraron shaidu da kuma bayanin wanda Eze na amsa laifin, ta yanke masa hukuncin.

Tirela murƙushe ’yan sanda 3 har lahira

An ƙwace kwantainoni 54 mallakin Emefiele

Fulawa da dabbobin Fadar Shugaban Ƙasa za su ci N125m a 2025

Za a rataye shi saboda kisan jariri