Za a rataye tsohon minista a Bangladesh kan laifin fyade

Wata kotu a kasar Bangladesh ta yanke wa tsohon ministan gona a kasar Syed Mohammad Kaiser hukunci kisa ta hanyar rataya bayan ta kama shi da laifin fyade da na kisan gilla.Tun a farko an tuhumi tsohon ministan da aikata laifin kisan gilla a 1971 a lokacin da kasar take fafutukar neman ’yanci daga kasar […]

Za a rataye tsohon minista a Bangladesh kan laifin fyade
Za a rataye tsohon minista a Bangladesh kan laifin fyade

Wata kotu a kasar Bangladesh ta yanke wa tsohon ministan gona a kasar Syed Mohammad Kaiser hukunci kisa ta hanyar rataya bayan ta kama shi da laifin fyade da na kisan gilla.
Tun a farko an tuhumi tsohon ministan da aikata laifin kisan gilla a 1971 a lokacin da kasar take fafutukar neman ’yanci daga kasar Pakistan.
Kaiser mai kimanin shekara 73 shi ne mutum na 15 da kotun ta yi wa shari’a a kasar, inda aka same shi da laifin jagorantar ’yan bindiga da suka kashe mutane 150 sakamakon wata takaddama a kasar.
Lauyoyin tsohon ministan sun ki amincewa da wannan hukuncin inda suka daukaka kara.
Gwamnatin Sheikh Hasina Wazed ta kafa wannan kotun a shekarar 2010 don tabbatar da shari’a a kan wadanda suka aikata manyan laifuffuka. Sai dai ana zargin kotun ta fi mayar da hankali wajen yi wa ’yan Jam’iyyar Jamaat-e-Islami shari’a.
Wadanda suka shigar da karar sun ce Kaiser ya hada gungun ’yan bindiga da ke goyon bayan Pakistan, inda suka rika kashe-kashe da fyade da kuma satar dukiyar jama’a.
Mai Shari’a Obaidul Hassan ya ce ya gamsu da nagartattun hujjoji da aka bayyana a gaban kotunsa cewa Kaiser ya aikata laifuffukan da ake tuhumarsa.
Wanda ya jagoranci wadanda suka shigar dakara mai suna Mohammad Ali, ya ce Kaiser ya jagoranci ’yan bindiga da jami’an tsaron Pakistan, inda suka kai hare-hare a kauyuka 22 a yankin Brahmanbaria da ke iyaka da kasar Indiya a Nuwamba, 1971.
“Akalla an kashe ’yan Hindu 108, an sace dukiyarsu, an kuma kona musu gidaje.” Inji shi.
Kaiser ya shiga jam’iyyar Jatiya a 1980, inda aka zabe shi dan majalisar dokoki. Shugaba Hussain Muhammad Ershad ya nada shi Ministan Gona.