Za a rataye wanda ya kashe mahaifinsa saboda Naira 56,000
Wata kotun daukaka kara da ke Jos babban birnin jihar Filato ta yanke wa wani matashi Jibril Idrisa hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda kashe mahaifinsa da ya yi akan dalilin mahaifin ya sayar da dawa da kudinta ya kai Naira dubu 56. Alkalin kotun Habib Abima ne ya yanke masa hukuncin kamar yadda doka […]
Rataya
Wata kotun daukaka kara da ke Jos babban birnin jihar Filato ta yanke wa wani matashi Jibril Idrisa hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda kashe mahaifinsa da ya yi akan dalilin mahaifin ya sayar da dawa da kudinta ya kai Naira dubu 56.
Alkalin kotun Habib Abima ne ya yanke masa hukuncin kamar yadda doka ta tanadar ga wanda ya aikata irin wannan laifin, kamar yadda kamfanin dillancin labarai NAN ya sanar.