Za a rataye wanda ya kashe mahaifiyarsa ta hanyar duka

Babbar kotun jihar Filato da ke Jos babban birnin jihar ta yanke wa wani matashi mai suna Godwin Banchir mai shekara 24 hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda lakada wa mahifiyarsa ‘yar shekara 65 duka har sai da ta mutu sakamakon rashin amsa gaisuwar da dan ya yi ma ta. Alkalin kotun Daniel Longji ne […]

Za a rataye wanda ya kashe mahaifiyarsa ta hanyar duka

Rataya

Babbar kotun jihar Filato da ke Jos babban birnin jihar ta yanke wa wani matashi mai suna Godwin Banchir mai shekara 24 hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda lakada wa mahifiyarsa ‘yar shekara 65 duka har sai da ta mutu sakamakon rashin amsa gaisuwar da dan ya yi ma ta.

Alkalin kotun Daniel Longji ne ya yanke wa Banchir hukuncin bayan an tabbatar da laifinsa akan kisan mahaifiyarsa mai suna Misis Saratu Banchir da ya aikata.