Za a rika daukar hoton yatsun ’yan majalisar Kenya da suka halarci zama
Majalisar Dokokin kasar Kenya ta kaddamar da wani shiri na daukar hoton yatsun wakilan majalisar da suka halarci zamanta.Sai dai Shugaban Majalisar, Justin Muturi ya musanta cewa an bullo da hakan ne domin a “dakile almundahana” inda ya ce an yi haka ne domin gaggauta rajistar sunayen da kuma tabbatar da tsaro.An yi ta zargin […]
Majalisar Dokokin kasar Kenya ta kaddamar da wani shiri na daukar hoton yatsun wakilan majalisar da suka halarci zamanta.
Sai dai Shugaban Majalisar, Justin Muturi ya musanta cewa an bullo da hakan ne domin a “dakile almundahana” inda ya ce an yi haka ne domin gaggauta rajistar sunayen da kuma tabbatar da tsaro.
An yi ta zargin ’yan majalisar da yin amfani da yaransu wajen sanya hannu a madadinsu yayin karbar Dala 58 (kimanin Naira dubu 10) a matsayin alawus din zama a majalisar ba tare da sun zauna ba.
’Yan majalisar Kenya na daga cikin ’yan majalisar da suka fi karbar albashi a duniya.
Wakilin gidan rediyon BBC a Nairobi babban birnin kasar, Odeo Sirari, ya ce ’yan majalisar sun shafe safiya wajen daukar hoto yatsunsu kafin bude zaman majalisar da rana bayan dawowa daga hutun Kirsimeti.
Mafi yawan ’yan majalisar sun yi murna da sabon tsarin, sai dai sun koka kan yadda ba a sanar da su kan bullo da tsarin ba, inji shi.
Muturi ya shaida wa ’yan majalisar cewa: “Ina son in yi gyara ga bayanan da kafafen watsa labarai ke bayarwa cewa an sanya na’urori ne domin a dakile almundahana a tsakanin ’yan majalisar.”
“Na’urorin za su rage bata lokaci, saboda yanzu ba za a bukaci ’yan majalisar su tsaya a layi domin su rika rubuta sunayensu da hannu ba,” inji shi.
Wakilin BBC ya ce an ba ’yan majalisar mako daya su yi rajistar sunayensu, daga nan sais u rika amfani da na’urar daukar hoton yatsu a yayin shiga majalisar wadda ake zamanta a ranakun Talata da Alhamis da rana, kuma a shafe yinin Laraba.